Mutum uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka jikkata, bayan da wata tankar mai ta muƙushe adaidaita sahu a Jihar Filato.
Hatsarin ya faru ne a kan titin Farin Gada da ke Jos ta Arewa, kusa da Gidan ɗaliban Jami’ar Jos.
- Ban yi nadamar cire tallafin man fetur ba – Tinubu
- Najeriya na kan turbar samun ci gaba mai ɗorewa — Tinubu
Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a jihar, Peter Yakubu, da Sakataren Ƙungiyar Agaji ta Red Cross, Nura Ussaini Magaji, sun tabbatar da faruwar lamarin.
Sun ce wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu sun yi raga-raga ta yadda ba a iya gane su.
“Abubuwa biyu ne suka yi taho-mu-gama – wata tankar mai da adaidaita sahu.
“Mutum uku sun mutu, sannan mutum huɗu sun samu raunuka a hatsarin,” in ji Yakubu.