A kokarinta na cike gibin ma’aikatan lafiyar masu fama da matsalar kwakwalwa a matakin farko, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe ta horar da ma’aikata 70 a bangaren.
Babban Jami’in Shirin Gaggawa na WHO a yankin Arewa maso Gabas, Dokta Richard Lako, ya ce an dade ana fama da rashin yin kasafin kudin da ya dace domin kula da masu matsalar a kusan ko’ina a duniya.
- Yoyon kwano: Ginin Majalisa ya dade yana neman gyara —Lawan
- Da yiwuwar PSG za ta dauki Ronaldo daga Juventus
“Gibin da ke kasafin masu matsalar kwakwalwa matsala ce da ta shafi duniya domin kasashe matsakaita da masu wadata ba su cika kula da tallafa wa bangaren ba, kashi biyu ne kawai ake ware wa bangaren kuma ya yi karanci,” inji shi.
Ya bayyana ta bakin wakilinsa kuma jami’in kula da sashin masu tabin hankali, Samuel Tarfa, cewa hakan ce ta sa WHO ta ga dacewar yin hadaka da Gwamnatin Yobe domin cike gibin, inda hukumar ta nemo ma’aikata 70 ta horar da su kan kula da masu lalurar.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Yobe, Dokta Muhammad Lawan Gana, ya ce horar da ma’aikatan jinya a matakin farko abu ne da ya dace.
Ya ce horon zai ba ma’aikatan lafiyar damar ganowa da kuma kula masu fama da matsalar kwakwalwa ta yadda ya dace, idan kuma abin ya fi karfinsu sai su tura masu matsalar zuwa inda ya dace.
Jami’in ya yi matukar godiya ga hukumar ta WHO bisa hadakar, da ta zakulo ma’aikata daga daukacin kananan hukumomi 17 na jihar ta Yobe.