✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma (6)

4.  Yafe kisasi:Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga dan uwansa, to a bi da alheri da biya zuwa…

4.  Yafe kisasi:
Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga dan uwansa, to a bi da alheri da biya zuwa gare shi da kyautatawa.” (k:2:178).
Ibnu Sa’adiy ya ce: “A cikinsa akwai saukakawa da kwadaitarwa wajen yin afuwa zuwa ga karbar diyya, kuma mafi kyawun haka, yin afuwa ba tare da karbar diyyar ba.” (Taisirul Karimir Rahman shafi na 67).
Sayyid kutub ya ce: “Wannan shari’a ba ta kasance abar halattawa ga Bani Isra’ila a cikin Attaura ba. Abin sani, an shar’anta ga al’ummar Musulmi domin kubutar da rayuka idan aka samu yarda da yafiya.” (Fi-Zilalil kur’an, mujalladi na 1 shafi na 164-165).
Kuma ya sake cewa: “Daga wannan za mu gane yalwar Musulunci da basirarsa wajen kare ran dan Adam a yayin shar’anta abubuwan da suka shafe ta da kuma saninsa ga abin da aka sanya ta a kai na jayayya. Lallai fusata kan zubar da jini fitira ce ta dabi’a, to amma sai Musulunci ya kwantar da ita ta hanyar tabbatar da shari’ar kisasi. Kuma cikakken adalci shi yake karya sharrin rayuka ya kwantar da kunci zukata ya tsoratar da dan ta’adda daga ci gaba da ta’addancinsa. Sai dai duk da haka Musulunci a lokaci guda yana kwadaitarwa wajen yin afuwa, yana bude masa, yana tsara masa haddodi. Sai ya kasance kira gare shi bayan tabbatar da kisasi, kira ne na samar da haddodi na tadawwa’i ba na faralci da zai wahalar da dan Adam ya dora masa abin da ba zai iya ba.” (Fi- Zilalil kur’an, mujaladi na 1 shafi na 164-165).

5. Haramcin kunar bakin wake
An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya hau dutse ya fado ya kashe kansa yana cikin wutar Jahannama, za a rika hawa da shi tsaunin a Jahannama a rika jefo shi a cikinta yana madawwami a cikin wannan hali har abada. A tare da shi akwai wanda ya sha guba ya kashe kansa, zai tashi da gubarsa a hannunsa yana sha a cikin Jahannama yana mai tabbata a haka har abada. Haka wanda ya kashe kansa da karfe (makami kamar wuka ko takobi ko bindiga ko bam) zai tashi da makaminsa a hannun yana sokawa a cikinsa a wutar Jahannama yana mai dawwama a haka har abada.” (Buhari, Kitabud dibbu, Babu Sharbus Sammi wad Dawa’i Bihi, Hadisi na 5778 da Muslim a Al-Iman, Hadisi na 109).
Kuma an karbo daga Sabitu bin Dahhak (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi rantsuwa da wani addini ba Musulunci ba, yana mai karya da gangan, to yana kamar yadda ya ce. Wanda ya kashe kansa da karfe (makami) da shi za a azabtar da shi a cikin wutar Jahannama.” (Buhari, Kitabul Jana’iz, Babu Ma Ja’a fi katlin Nafsi, Hadisi na 1363 da Muslim a Al-Iman, Hadisi na 110).  
Annawawi (RH) ya ce “A cikin wadannan Hadisai akwai bayanin gargadi mai tsanani wajen haramta kashe kai.” (Sharhu Sahihul Muslim, mujalladi na 2 shafi na 125).
“Lallai mutum ya wajaba ya sani shi mallakar Mahaliccinsa ne, ba shi ya mallaki kansa ba. Don haka ba ya halatta ya sarrafa komai game da kansa face a bisa haddodin da Mahaliccinsa Ya yi masa izini. Ba ya da ikon ya cutar da kansa bisa hujjar ai bai yi ta’addanci ga wani ba. Domin ta’addanci a kansa, kamar ta’addanci ne a kan waninsa a wurin Allah Madaukaki.” (Al-Islam wad Daruratil Hayat, shafi na 54).
Babbar magana, idan laifi ne mutum ya halaka kansa shi kadai bisa kowane dalili, to ina ga mutum da zai dauki makami ya yi ta’adda ya halaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba da sunan kunar bakin wake? Ina matsayin mutum da zai je ya ajiye bam a inda zai halaka ran wasu daban, wadanda in da Allah zai tuhume shi ya fadi laifin da suka aikata na cancantar hakan ba zai iya fada ba?
Idan mutum a kashin kansa an haramta masa ya halaka kansa, yaya zai yi da jinin mutanen da ya kashe ba tare da sun aikata wani laifi da shari’a ta yanke musu hukuncin kisa ba?
Musulunci ba bagidajen addini ba ne da zai ce a shiga kasuwa a rika kisan kan mai uwa da wabi da sunan addini! Duk wanda ya aikata haka ba Musulunci yake yi ba, sai dai ya je ya nemi addinin da ya umarce shi da yin haka!

6. Halatta haram saboda lalura:
Allah Madaukaki Ya ce: “Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da naman alade da wanda aka ambaci sunan wanin Allah game da shi, sa’annan wanda aka tilasta, ba yana mai wuce iyaka ba (in ya ci), to, lallai Allah Mai gafara ne, Mai jinkai.” (k:16:115).
Kuma Madaukaki Ya ce: “Hakika Ya rarrabe muku daki-daki, abin da Ya haramta a kanku, face fa abin da aka bukatar da ku (ya zama tilas) bisa lalura zuwa gare shi.” (k:6:119).
Ibnu Jarir ya ce: “Wanda lalurar yunwa ta sanya shi cin abin da aka haramta na daga mushe da naman alade da abin da aka ambaci sunan wanin Allah (wajen yanka shi), babu komai a kansa cikin abin da ya ci, idan ya ci.” (Jami’ul Bayan, mujalladi na 2 shafi na 91).
Ibnu Kathir ya ce: “Hakika an bayyana muku abin da aka haramta a kanku, kuma an yi bayaninsa dalla-dalla, face a halin matsuwa, to lallai yana halatta muku ku ci abin da kuka samu.” (Tafsirul kur’anil Azim, mujalladi na 2 shafi na 174).
Ibnu Hazmi ya ce: “Duk abin da Allah Madaukaki Ya haramta na daga abin ci da na sha, kamar naman alade ko ababen farauta na haram ko mushe ko jini ko naman dabbobi masu dagi da sauransu, dukkansu a yayin lalura halal ne, amma ban da naman dan Adam komai lalura. Kuma wanda matsuwa ta sa shi cin daya daga cikin abubuwan da muka ambata kuma bai samu wata dukiya daga jama’ar Musulmi ko abokan amana ba, yana iya ci har ya koshi, kuma ya yi guzuri da shi har sai ya samu halal. Idan ya same ta, sai halal ta koma haram, kamar yadda ta kasance yayin gushewar lalurar.” (Almuhalla, mujalladi na 7 shafi na 426).
Daga abin da ya gabata, abubuwa biyu sun bayyana ga rai kamar haka:
1.    Halatta abubuwan da aka haramta saboda lalura, kuma an yi bayani a kansa a sama.
2.     Wajibcin baza dukiya ga wanda yake cikin matsi domin kubutar da rayuwarsa daga halaka.
Annawawi (Rahimahullah) ya ce: “Idan ya zamo mamallakin abinci ba matsattse ba ne, ya lizimce shi ya ciyar da matsattse, Musulmi ne ko zimmi ko wanda aka karbi amanarsa. Kuma matsattse yana iya karbar abincin da karfi ko da zai kai ga fada da mai mallakar, kuma ko da ya kashe mai mallakar, diyya ba ta lamunce shi ba, amma da mai mallakar abincin zai kashe matsattsen domin kare abincinsa, kisasi ya lizimce shi.” (Almajmu’u, mujalladi na 9 shafi na 48).