✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lalurori biyar da suka wajaba shugabanni su tsare su ga al’umma 12

6. Haramcin zina da wajibcin haddi a kanta:Allah Madaukaki Ya ce: Kuma kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta…

6. Haramcin zina da wajibcin haddi a kanta:
Allah Madaukaki Ya ce: Kuma kada ku kusanci zina. Lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munanan ga zama hanya.” (k:17:32).
Ibnu Jarir ya ce: “Hanyar zina ta munana hanya, domin ita hanya ce ta ma’abuta sabo da masu saba umarnin Allah. Kuma mafi munin hanyar tana tunkuda mai bin ta zuwa cikin wutar Jahannama.” (Jami’u ma’al Bayan, mujalladi na 15, shafi na 80).
Ibnu Sa’adiy kuma ya ce: “Allah Ya siffanta zina kuma Ya munana ta ta fadin cewa, ta kasance alfasha, ma’ana babu abin da take yi ban da bata shari’a da hankali da fidira, saboda ta kunshi keta hurumin hakkin Allah da hakkin matar da iyalanta ko mijinta da fasadi a kan shimfidarta da gaurayar nasabobi da sauran wasu fasadodi.” (Taisirul Karimir Rahman, shafi na 456).
Hakika shari’a ta wajbta yin haddi a cikin aikata wannan aiki na mujirimanci. Allah Madaukaki Ya ce: “Mazinaciya da mazinaci, to ku yi bulala dari ga kowane daya daga gare su.” (k:24:2).
An karbo daga Ubbadatu bin Samit (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku rika daga gare ni, hakika Allah Ya sanya musu mafita. Budurwa da saurayi bulala dari da kora (dauri) na shekara daya. Bazawara da bazawari bulala dari da jefewa.” (Muslim a Kitabul Hudud).
Sheikhul Islam ya ce: “Amma mazinaci idan ya kasance ya taba aure, to lallai ne ana jefe shi da duwatsu har sai ya mutu, kamar yadda Annabi (SAW) ya jefi Ma’iz bin Malik Al-Aslami kuma ya jefe Algmidiyya da sauransu. Kuma Musulmi suka yi rajamu a bayansa. Idan ya kasance bai yi aure ba, sai a yi masa bulala dari da Littafin Allah kuma a daure shin a shekara daya da Sunnar ManzonSa (SAW).” (Majma’u fatwa mujalladi na 28, shafi na 333).
Kuma daga cikin makasudodin shari’a na haramta zina akwai:
1. Tabbatar da bauta ga Allah Madaukaki da tsayuwa kan shari’arSa.
2. Tsarkakae mukallafi daga zunubai da laifuffuka da gargadi ga waninsa kada ya auka musu.
3. Tsare daidaikun mutane da daukacin jama’a. (Hukumuz Zina fil kanuni wa Alakatiha bi Mabadi’i Hukukil Insani fil Garbi, shafi na 42).
7. Haramcin luwadi da wajibcin yin haddi kansa:
Shekhul Islam ya ce: “Amma luwadi daga cikin malamai akwai mai cewa: “Haddinsa kamar haddin zina ne. Kuma an ce: “Bai kai haka ba.” Amma ingantaccen abin da sahabbai suka hadu a kansa a kasha su biyu na saman da na kasan, shin sun taba aure ko ba su taba yi ba. Kuma ma’abuta Sunan sun ruwaito daga Ibnu Abbas (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Wanda kuka same shi yana aiki irin na mutanen Ludu kun kasha mai yi da wanda ake yi da shi.” (Abu Dawud a Hudud Hadisi na 4462 da Tirmizi a Hudud, Hadisi na 1457 da Ibnu Maja a Hudud, Hadisi na 2561). Kuma Abu Dawuda ya ruwaito daga Ibnu Abbas (RA) kan saurayin da aka samu yana luwadi ya ce: “Za a yi masa rajamu.” (Abu Dawuda a Hudud, Hadisi na 4463). Sahabbai ba su yi sabani kan kasha shi ba, sai dai nauyin kisan. Domin an ruwaito daga Siddik (RA) cewa ya yi umarni da a kone shi. Waninsa kuma ya ce a kashe shi, wasu kuma suka ce a rika rusa masa bangon gini har sai ya mutu a karkashin ginin. … wasu sun ce a hau da shi saman gini (ko dutse) a cikin alkarya a turo shi kasa sannan a biyo shi da jifa da duwatsu kamar yadda Allah Ya yi ga mutanen Annabi Lud. Wannan ruwayar an same te daga Ibnu Abbas. Wata ruwayar ta ce: “A jefe shi da duwatsu. Kuma a kan haka mafi yawan magabata suke. Suka ce: “Saboda Allah Ya jefe mutanen Lud ne, sai Ya shar’anta jefe mazinaci don kamantawa da mutanen Lud, don haka sai a jefe su biyun ya alla sun kasance ’ya’ya ne ko bayi ko dayansu bawa daya da matukar dai sun kasance baligai. Idan dayansu bai balaga ba, sai a yi masa wata ukubar da ba ta kai ta kisa ba, ba a jefe mutum sai wanda ya balaga.” (Majmu’ul Fatawa, mujalladi na 28, shafi na 334 -335).
8. Haramcin kazafi da wajibcin haddi kansa:
Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne wadannan da suke jifar mata masu kamun kai gafilai, muminai, an la’ane su a cikin duniya da Lahira, kuma suna da azaba mai girma.” (k:24:23).
Ibnu Kasir ya ce: “Wannan gargadi da tanadin narko daga Allah Madaukaki ga wadanda suke kazafi ga mata masu kamun kai, gafilai, muminai ne.” (Tafsiru kur’anil Azim, mujaaladi na 3, shafi na 287).
kazafi babban zunubin ne daga cikin manyan zunubai da nassi ya yi magana a kansu.
An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Ku guji abubuwa bakwai masu halakarwa.” Suka ce: “Ya Manzon Allah wadanne ne?” Ya ce: “Shirki da Allah da sihiri da kasha rai wanda Allah Ya katange face da hakkin shari’a da cin riba da cin dukiyar maraya da juya baya lokacin da yaki ya rincabe a fagen daga da kuma jifar mata masu kamun kai, gafilai, muminai da zina.” (Buhari a Kitabul Hudud da Muslim a Kitabul Iman).
Hafiz ya ce: “A cikin ayar akwai bayanin kasancewar kazafi na daga cikin kaba’irai dogaro da cewa duk abin da aka yi tattalin la’ana da azaba a kansa, ko aka shar’anta haddi  a kansa, to babban laifi ne. Don haka ne Hadisin ya dace da ayar da aka ambata. Kuma an yi ittifaki cewa yin kazafi ga namiji mai kamun kai hukuncinsa daidai ne da hukuncin yin kazafi ga mata masu kamun kai.” (Fathul Bari, mujalladi na 12, shafi na 188).
Don haka ne Allah Madaukaki Ya hukunta haddi a kan wannan mugun aiki domin tsare mutuncin muminai maza da mata. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wadanda ke jifar mata masu kamun kai, sa’annan ba su kawo shaidu hudu ba, to, ku yi musu bulala, bulala tamanin, kuma kada ku karbi wata shaida tasu har abada. Wadancan su ne fasikai.” (k:24:4).
Ibnu Kasir ya ce: “Wannan aya mai girma a cikinta akwai bayanin hukuncin yin bulala ga mai kazafi ga mace mai kamun kai, ita ce ’ya, baliga, mai kamun kai. Idan wanda aka yi wa kazafi namiji ne, haka za a yi bulala ga wanda ko wadda ta yi masa kazafi. Babu sabani a tsakanin malamai a cikin hakan.” (Tafsirul kur’anil Azim, mujalladi na 3, shafi na 275). Kuma ya kara da cewa: “An wajabta wa mai kazafi idan ya kasa kawo shaidar tabbatar da abin da ya fada, hukunce-hukunce uku: Na farko a yi masa bulala tamanin. Na biyu a daina karbar shaidarsa har abada. Na uku ya zama fasiki ba mai adalci ba, a wurin Allah da wurin mutane.” (Tafsirul kur’anil Azim, mujalladi na 3, shafi na 275).
Shekhul Islam ya ce: “Daga cikin haddodin da Alkur’ani da Sunnah suka zo da su, kuma Musulmi suka hadu a kansu akwai haddin kazafi. Idan wani mutum ya yi kazafi ga mai kamun kai da yin zina ko luwadi, haddin bulala tamanin ya wajaba a kansa, mai kamun kai a nan shi ne da mai kamun kai.”  (Majmu’ul Fatwa, mujalladi na 28, shafi na 342).
 “Kuma a cikin kazafi akwai zubar da kimar namiji ko matar da ake tuhuma da iyalansu da makusantansu da ita kanta al’umma. A cikinsa akwai sukar nasbar dan da aka tuhumci uwarsa da zina, don haka shari’a ta zo tana haramta shi tare da wajibcin yin haddi a kansa domin kare martabar daidaikun jama’a da al’umma kanta.” (Al-Islam wa Daruratil Hayat, shafi na 103 -104).