Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya janye dokar hana fita ta sa’a 24 da ya sanya a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da ke jihar daga ranar Laraba.
Gwamnan ya janye dokar ne da yammacin Talata, bayan nazarin da Majalisar Tsaron jihar ta yi kan kwanciyar hankalin da aka samu a jihar.
- Ba za mu bari Filato ta sake fadawa cikin rikici ba – Lalong
- Lalong ya kafa kotun hukunta ‘barayin’ tallafin COVID-19 a Filato
A ranar Asabar Lalong ya sake dawo da dokar hana fita ta sa’o’i 24, wadda da farko ya sassautata ranar Juma’ar, saboda fasa wuraren ajiye kayan abinci da wawushe su da wasu matasa suka yi a ranar ta Asabar.
Saboda haka gwamnatin ta dawo da dokar, don dakile wadannan fashe-fashe na rumbunan ajiye kayan tallafin.
Gwamnan ya shawarci al’ummar jihar su ci gaba da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba, kuma jami’an tsaro za su ci gaba da yin sintiri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma umarci jami’an tsaron da su damke duk wani wanda ke kokarin kai hari kan dukiyoyin jama’a a jihar da sunan zanga-zanga.