✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lallai Allah Yana son masu takawa

Daga Hudubar Malam Muhammad Awwal  HashimNa’ibin Limamin Masallacin Garejin Utako, Jabi, Abuja Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccina, ya Masoyin masu amsa kira! Ya Mai…

Imam Muhammad Awwal HashimDaga Hudubar Malam Muhammad Awwal  Hashim
Na’ibin Limamin Masallacin Garejin Utako, Jabi, Abuja

Godiya ta tabbata ga Allah Mahaliccina, ya Masoyin masu amsa kira! Ya Mai natsar da zukatan wadanda ke cikin dimuwa! Ya Mai amintar da masu tsoro! Ya Mai karbar masu tuba! Kuma ya Mafi rahamar masu rahama. TsarkinKa ya tabbata! Ka datar da talikai ga yi maKa da’a, kuma aikinsu abin godewa ne. Ka tabbatar da burin masu buri da rahamarKa, kuma Ka ba su kyauta mai yawa. Ka shimfida karmicinKa shimfidawa ga masu tuba, sai zunubinsu ya wayi gari abin gafartawa.
Kai ne Makadaici wanda ya nufi waninKa ya bata. Kai ne Mabuwayi wanda ya nemi waninKa ya kaskanta. Kuma Kai ne Ka kadaita da siffofin kamala kuma Ka daukaka da girman daraja.
“Ya Makadaici a mulkinSa da bai da na biyu,
Ya Wanda idan na ce, ‘Ya Maulana!’ Yake amsa mini.
Ina sabonka Kana suturce ni, na manta Ka, Ka tuna ni,
Yaya zan manta Ka, Ya Wanda bai manta ni!”
Na shaida lallai shubanamu Annabi Muhammad bawan Allah ne ManzonSa kuma AnnabinSa zababbe, ManzonSa zababbe, mafi alherin wanda sama ta yi wa rumfa, kuma jagoran masu takawa, shugaban mutanen farko da na karshe, wanda ya ce game da kansa: (Misalina da misalin Annabawan da suka gabace ni, kamar mutum ne ya gina gida ya kyautata shi ya kawata shi, sai dai ya bar gurbin tubali (bulo) daya daga wani bangare na ginin, sai mutane su rika zagaya shi suna mamakinsa, suna cewa, ‘ina ma an sanya wannan tubali!’ To ni ne wannan tubali, kuma ni ne cikamakin Annabawa.”
Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a gare shi a cikin mutanen farko da na karshe da kuma a cikin sama har zuwa Ranar kiyama.
Bayan haka, masoyana saboda Allah, ina rokon Allah Mai girma, Ubangijin Al’arshi Mai daraja bisa baiwarSa da kyautarSa da karimcinSa, Ya tayar da ni da ku tare da bayinSa masu takawa da salihai da sahabban Annabinmu amintacce (SAW). Muna kuma rokon Allah Ya dandana mana zakin takawa da imani da yakini da ikhlasi a cikin zukatanmu. Kuma muna neman tsarin Allah daga shamakance su a tsakanin zukatanmu. Muna rokonSa Ya hada mu tare da masoyin zukatanmu, Muhammad (SAW). Kuma muna rokonSa Ya haskaka gannanmu, Ya tafiyar da bakin cikinmu da damuwarmu, ta sanya mu a cikin (Aljannar) Firdausi mafi daukaka, Shi ma’abucin haka ne, kuma Mai iko a kansa.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Kuma kyakkywar karshe ta masu takawa ce.
Bayan haka, ya ku ma’abuta tauhidi masu girma! A yau muna wani wa’adi na ganawa ne, kuma ganawarmu a yau mai albarka ce, za mu yi magana ne a kan wani nau’i daga cikin nau’o’in mutane da Allah Mai tsarki da daukaka Yake so. Wannan nau’i ne na wadanda Allah Mai tsarki da daukaka Ya yi musu alkawari mai girma. Wannan nau’in ba su dandanar zafin fitina ko jarrabawa face suna da mafita, tsanani bai taba sauka musu ba, face tare da shi akwai sauki. Bakin ciki bai taba bayyana gare su ba, face Allah Mai tsarki da daukaka Ya kwaranye musu. Wata matsala ba taba samunsu a ce duniya duk da fadinta ta yi musu kunci ba, face (Allah) Ya sanya musu kofa da mafita. Shin kun san su wane ne wadannan? Ko kun san su wane ne wadannan? Su ne masu takawa (masu tsoron Allah ta kiyaye dokokinSa). “Kuma wanda Ya ji tsoron Allah Zai sanya masa mafita. Kuma Ya azurta shi ta inda ba ya zato. Kuma wanda ya yi tawakkali ga Allah,to, Shi (Allah) Ya isar masa.” (Suratud  dalaki).  Lallai su abin so ne. “Lallai Allah Yan son masu takawa.” (Suratut Tauba).
An yi ta maimaita soyayyar Allah ga masu takawa a wurare da yawa a cikin Alkur’ani Mai girma.
Wuri na farko a cikin fadinSa Mai tsarki da daukaka. “Tabbas wanda ya cika alkawarinsa kuma ya yi takawa, to, lallai ne Allah Yana son masu takawa.” (Suratu Ali Imrana).
Na biyu: Cikin fadinSa Madaukaki kan mushirkan Makka. “Abin da suka tsayar muku (na amana) kuma ku tsayar musu. Lallai ne Allah Yana son masu takawa.”
Na uku: FadinSa Madaukaki a kansu har wa yau: “Kuma ku cika musu alkawarinsu zuwa ga wa’adinsa. Kuma masu takawa su ne masu cin nasara.”
Su ne masu samun rahama, su ne wadanda ake taimako, su ne wadanda babu tsoro a kansu kuma ba su yin bakin ciki, kamar yadda Ubangijinsu Mai girma da daukaka Ya ba da labari a kansu: “To wanda ya yi takawa kuma ya kyautata, babu tsoro a kansu, kuma ba su yin bakin ciki.” (Suratul A’arafi).
Mece ce takawa? Kuma wadanne ne siffofin masu takawa? Kuma mene ne alamomin takawa?
Ibnu Al-Mu’utazzi ya siffanta ta a cikin wasu baitocinsa siffantawa cikakkiya, sai ya ce:
“Barin yin zunubai kananansu,
Da manyansu, wannan ne takawa.
Ka yi kamar mai tafiya a kasa,
A tsakanin kayoyi yana saunar abin da yake gani.
Kada ka raina karaminsa (zunubi),
Domin duwatsu daga tsakuwa suka faro.”
Ibnu Habib ya fassara takawa da cewa: “Takawa ita ce, ka yi aiki bisa da’a ga Allah a bisa haske daga Allah (ilimi) don fatar rahmar Allah (cikin ikhlasi). Kuma ka bar saba wa Allah a bisa haske daga Allah kana mai tsoron ukubarsa.”
Takawa ta kunshi dukkan alheri, ita ce wasiyyar Allah Mai tsarki da daukaka ga mutanen farko da na karshe. “Kuma hakika lallai, Mun yi wasiyya ga wadanda aka ba su Littafi a gabaninku da kuma ku, cewa ku yi takawa (jin tsoro) ga Allah.” (Suratu Nisa’i).
Ita ce mafi alherin abin da mutum zai amfana da shi, kamar yadda Abu Darda’i (RA) ya ce. Hakika an ce masa: “Lallai abokanka sun yi wakoki, amma kai ba abin da aka samu daga gare ka.” Sai ya rera cewa:
“Mutum yana son burinsa ya cika,
Amma Allah Ya ki, sai abin da Ya nufa.
Mutum yana cewa fa’idata da dukiyata,
Amma takawar Allah ce mafi falalar rabauta.”
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmi. Ka kaskantar da kafirci da kafirai.
Ya Allah! Ka ba mu zaman lafiya a kasarmu da sauran kasashen Musulmi. Ya Allah Ka kara tsira ga shugabanmu Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi tsira a kan Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim. Lallai ne Kai Abin godewa ne Mai girma. Ya Allah! Ka kara aminci a kan shugabanmu Annabi Muhammad da alayen Annabi Muhammad, kamar yadda Ka yi aminci a kan Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim. Lallai ne Kai Abin godewa ne Mai girma.