✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Lalata ’yar makwabci ya sa kotu tsare dan acaba

Kotun ta bayar da umarnin a mika fayil din kes dinsa zuwa ofishin gurfanar damasu laifi na gwamnatin jihar

Kotun Majistare da ke Ikeja a Jihar Legas ta tsare wani mai sana’ar acaba mai shekara 33  da ya yi fyade ga ’yar makwabcinsa.

Alkaln kotun, Misis B.O. Osunsanmi, a bayar da umanin ne bayan an gurfanar da matashin a gabanta ranar Alhamis kan zargin aikata fyade.

Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa a ranar 2 ga watan Satumba ne wanda ake zargin a zakke wa karamar yarinyar mai shekara 10 a gidansa da ke unguwar Ikorodu.

Bayan umarnin tsare dan acaban, kotun ta bayar da umarnin a mika fayil din kes dinsa zuwa ofishin gurfanar damasu laifi na gwamnatin jihar.

Daga nan ta daage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba da muke ciki.