Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi.
Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa waɗanda maharan suka yi raunin harbi suna samun kulawa a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.