Shugaban Sashen Kimiyyar Kwamfuta na Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, Injiniya Bello Atiku tare ’ya’yansa biyu sun kubuta daga hannun wanda suka yi garkuwa da su bayan kwana tara da faruwar lamarin.
Kakakin kwalejin, Abdallah Shehu ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.
- Tsohon lakcaran KADPOLY ya harbi matarsa ya kashe kansa
- ’Yan bindiga sun sace lakcara da yara 2 a Zariya
- ’Yan bingida sun yi garkuwa da Rabaran a Abuja
- Masu garkuwa sun sako dalibai da malamarsu a Kaduna
“Yanzu haka sun kubuta kuma suna bukatar hutu.
“Ba mu da wani bayani game da halin da suka shiga, amma da zarar mun tattauna da su zamu sanar da ’yan jarida abin da ya faru”, inji Shehu.
Aminiya ta rawaito cewa a ranar 14 ga watan Nuwamba 2020, ’yan bindigar suka shiga rukunin gidajen malamai a kwalejin suka yi garkuwa da malamin suka kuma harbi makwabcinsa a hannu.
Yin garkuwa da mutane musamman a yankin Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare yana kuma kara kamari.
Ana kara shiga fargaba saboda yadda jihohi irinsu Kaduna, Katsina, Kebbi, Zamfara, Sokoto da sauransu ake shiga har gida a yi awon gaba da mutum ko a kashe shi.