Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya yi kira da a soke rijistar ’ya’yan jam’iyyar APC da ake gudanarwa a halin yanzu a Jihar Kwara.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ’yan jarida ranar litinin a mahaifarsa dake Oro, inda ya yi zargin cewa jami’an da aka tura don yin rijistar jam’iyyar a jihar sun karya ka’idojin da uwar jam’iyar ta kasa ta shimfida.
- Yadda aka yi hatsarin jirgin kasa a Legas
- An sa gasar kwaikwayon daurin dankwalin Ngozi Okonja-Iweala a Twitter
Ministan ya kuma ce kwamatin ya karya sharudan da aka gindaya na rarraba kayan gudanar da aikin rijistar ’ya’yan jam’iyyar a fadin jihar.
“Ka’idojin yin rijistar da uwar jam’iyyar ta shimfida a bayyane suke, kuma an haramta ba mutanen da basu da alaka da aikin kayan yin rijistar jam’iyyar su rarraba ko rike wasu muhimman takardu da foma-fomai da katinan jam’iyyar ga mutanen da ba su da ce a basu ba”
“Kayan aikin yin rijistar da suka hada da foma-fomai da kundin rijistar da katin shaidar zama dan jam’iyya wanda take jami’in yin rijistar a hukumance ne kadai ke da alhakin daukar bayanan mutum da rarraba katin kamar yadda aka tsara a hukumance,” In ji shi
Ministan ya bukaci a soke baki dayan rijistar a fadin Jihar ta Kwara har sai an tabbatar da yin rijistar kamar yadda jam’iyyar ta tsara kuma yadda kowa zai gamsu da tsarinta.