✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An harbe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah a Kwara

A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan sanda sun zo sun fara bincike.

Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin.

Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi.

“A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan sanda sun zo sun fara bincike.”

Sai dai mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kwara, Ejire Adeyemi Toun da wakilinmu ya tuntuɓa, ta buƙaci ya ba ta lokaci za ta waiwaye shi daga baya.

Bayanai sun ce marigayin mai shekaru 32 tsohon hadimi ne a wurin Shugaban Ƙaramar Hukumar Moro kuma ɗaya daga cikin shugabannin Matasa Fulani a Jihar Kwara.