✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari kan makiyaya an kashe shanu da dama a Filato

'Yan bindigar sun kai harin yankin inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya sa makiyayan suka gudu suka bar shanunsu.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan makiyaya a yankin Heipang da ke Ƙaramar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato a safiyar Laraba, inda suka kashe shanu da dama tare da jikkata wasu da dama.

A cewar shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Babayo Yusuf, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin a garin Jos, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari yankin inda suka fara harbe-harbe, lamarin da ya sa makiyayan suka gudu suka bar shanunsu.

Ya bayyana cewa an kashe shanun ne a lokacin da ake kiwonsu a yankin, inda ya yi Allah-wadai da harin wanda bai dace ba.

Shugaban ya ce sun kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an ‘Operation Safe Haɓen’, jami’an tsaro a yankin waɗanda suka yi musu rakiya zuwa inda lamarin ya faru tare da shawartarsu da su kwantar da hankalinsu.

Yusuf ya ce “Jami’an tsaro sun tabbatar mana da cewa za su binciki lamarin tare da kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aikar. Sun kuma yi gargaɗin a guji ɗaukar doka a hannu. Sun ce za su ɗauki matakin zaƙulo waɗanda suka kai harin.”

Shugaban Ƙungiyar MACBAN ya buƙaci mambobinsa da su kwantar da hankalinsu, tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa jami’an tsaro za su gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.

Har yanzu dai dukkan masu magana da yawun rundunar tsaro ta  ‘Operation Safe Haɓen’ da ‘yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom da DSP Alabo Alfred, ba su amsa tambayar da wakilinmu ya aika musu ba dangane da harin.