Wata Babbar Kotun Jihar Kwara, ta yanke wa wasu mutum biyar da ake tuhuma da fashi da makami hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai Shari’a Haleema Salman ta Babbar Kotun da ke birnin Ilorin ce ta yanke wa mutanen biyar da aka zarga da fasa bankin Offa shekaru shida da suka gabata.
- Sojoji sun kashe shugabannin ’yan bindiga 65 da mayaƙa 1,937 a watanni uku
- Sanata ya raba tallafin awaki a Kaduna
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 5 ga watan Afrilun 2018 ne ’yan fashi suka kai hari bankin a yankin Ƙaramar Hukumar Offa, inda suka kashe mutum 32 ciki har da ’yan sanda tara.
Kotun ta samu mutanen da laifin fashi da makami da kisan mutanen da ba su ji ba su gani ba, ciki har da jami’an ’yan sanda a lokacin mummunan harin.
Waɗanda hukuncin ya shafa sun haɗa da Ayoade Akinnibosun da Azeez Salahudeen da Niyi Ogundiran da Ibikunle Ogunleye da Adeola Abraham.
Jagoran lauyoyin da ke gabatar da ƙara, Rotimi Jacob (SAN), ya ce shekaru shida da suka shafe domin tabbatar wannan tuhumar sun haifar da ɗa mai ido.
Shi ma lauyan masu kariya, Nathaniel Emeribe wanda Abdullahi Jumba ya wakilta, ya ce hukuncin da kotun ta yanke bai zo da mamaki ba la’akari da irin ƙwararan hujjojin da aka gabatar a yayin shari’ar.
Da farko an tsara yanke hukuncin ranar 2 ga watan Agusta, amma sai aka jinkirta shi sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a faɗin Nijeriya.