✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA NA MUSAMMAN Cutukan zuciya da akan haifi jarirai da su

Ko za a yi min bayanin ciwon zuciyar da akan haifi wasu jariran da su?Amsa: Irin wadannan nau’uka na ciwon zuciya yakan rabu kashi biyu:…

Ko za a yi min bayanin ciwon zuciyar da akan haifi wasu jariran da su?
Amsa: Irin wadannan nau’uka na ciwon zuciya yakan rabu kashi biyu: Mai tsanani da maras tsanani. A mai tsananin sosai, wasu ma jariran ba sa kwana, da an haife su suke komawa. A nau’in da ba ya da tsanani kuma, jariri kan girma da shi ya kai munzalin babban mutum ba tare da ma an gane ba. Tsohon dan kwallon kafar nan na kasar nan Nwankwo Kanu, ba a san yana da irin wannan nau’i ba sai da ya girma.
An yi kiyasin cewa a cikin cutuka na nakasa da ake haifar yara da su, ciwon zuciya shi ne kan gaba domin akwai ire-irensa fiye da ashirin. A kalla jariri 1 a cikin jarirai 100 da ake haifa kullum, yana dauke da wannan matsala.
Babban abin da aka danganta da cewa shi kan kawo wannan ciwo shi ne nakasar ’ya’yan halittu na gado na zuciya, wadanda ke taimakawa wajen tsara halittar ita kanta zuciyar tun jariri na ciki. Su wadannan kananan halittu na gado da ake kira ‘genes’ sukan samu nakasa, wadda kan sa a samu aibu ko tangarda a yayin da zuciyar ke girma. To me ke kawo nakasar su kansu ’ya’yan halittun kuma? Bincike ya nuna cewa lahani kan faru ga wadannan ’ya’yan halittu idan mace ta gamu da wani ciwo wanda kwayoyin cuta kan kawo, musamman kwayar cutar ‘birus’ a lokacin da take dauke da juna biyu. Wato dai kwayoyin cuta sukan iya lahanta wadannan ’ya’yan halittu na jikin uwa da ma na jariri. Ya fi nunawa a jikin jariri, saboda shi ne sassan jikinsa ke da rauni.
Abu na biyu da aka danganta wannan matsala da shi shi ne shan magunguna barkatai da wasu masu juna biyu kan yi, walau na Bature ko na gargajiya, domin wasu magungunan guba ne ga wadannan halittu na gado ko halittun da ke zama sassan jiki a jarirai. Na uku akwai ruwan barasa, domin ita ma an tabbatar da lahanin da take wa ’ya’yan halittu na yaron da ke ciki. An fi samun irin wannan nau’i a irin kasasshen da mata ke dirkar barasa. Kai har ma hayakin taba sigari kan iya kawo wannan matsala. Wato kamar mai gidan da yake shan sigari a daki a gaban matarsa mai juna biyu. Duk wadannan suna taba lafiyar abin da ke ciki ne idan sun shiga mahaifa, domin ta nan jariri ke samun abinci da abin sha. Sai kuma ciwon suga idan mai ciki na da shi, wanda shi ma aka alakanta shi da lahani ga wadannan kwayoyin halittu na gado.
Bari mu dauki kadan daga cikin muhimman misalai na ire-iren ciwukan zuciya da ake haifar jarirai da su, mu ga yadda a akasarin lokuta suke sa aikin zuciyar ya rikice:
1.    A jarirai masu wannan ciwo za ta iya kasancewa maimakon zuciyarsu ta rabu gida hudu, su tasu gida uku ce ko biyu.
2.    Za ta iya kasancewa zuciyar na da huda ko kofa tsakanin bangaren dama da bangaren hagu, a gidan sama ko na kasa, wato babu tsokar naman da ta raba wadannan bangarori. Kuma da yake aikin bangaren dama daban da na hagu, in haka ta faru, jinin da ya kamata ya tafi huhu, sassa ko gangar jiki za shi, haka ma jinin da ya kamata ya bi gangar jiki, huhu zai je, ko kuma su gurbata da juna.
3.    Za ta iya kasancewa manyan magudanan jini, wato wadda take barin zuciya da kuma wadda ke dawowa zuciya su yi musaya a gidajen da ba nasu ba,
4.    Ko kuma su wadannan manyan magudanan jini su tsuke ta yadda jini ba zai fita da sauri ba, ko su samu huda.
5.    Za ta iya kuma kasancewa murafan da ke tsakanin gidan sama da na kasa su tsuke su hana zuciyar buga jini yadda ya kamata.
  Wasu a cikin irin wadannan, sukan sa a rasa yaro tun yana jinjiri, wasu kuma yaro yakan girma da su, amma sukan ba shi wahala, wasu kuma yaran sukan girma da ciwon ba tare da an ma gane ba. Kai wata nakasar ma da ikon Allah da kanta take gyaruwa in yaro na girma, kamar ’yar huda karama za ta iya hadewa.
Alamun Irin Wannan Nau’in Ciwo
Alamun da za a iya gani a ce jariri na da wannan ciwon ya danganta da tsanani ko rashin tsananin ciwon da kuma ko wane iri ne, kamar yadda muka kawo misalai a sama. Wani lokaci ba wata alama da ake gani, kuma hakan na nufin yaro zai iya rayuwarsa lafiya sumul. Wani lokaci kuma, akan ga wasu alamu ko ma a rasa yaron cikin kankanen lokaci ko watanni.
Alamun duk kusan iri daya ne, amma idan likita ya yi aune-aune da gwaje-gwaje, zai iya tantance ko wane iri ne. Alamun sun hada da yawan haki a jarirai; ko a ga ba sa iya shan mama sosai, sai dai su sha kadan su huta, sannan su kara sha; ko a ga lebbansu suna duhu ko baki-baki maimakon ja; ko a ga suna yawan zufa ko ba zafi. Za kuma a iya ganin kirjinsu yana bal-bal saboda saurin da zuciyar ke yi wajen bugawa. Idan yaro ya fara magana, yakan ce yana jin ciwon kirji, kuma za a ga bai cika shiga wasanni irin na yara ba, don ko ya shiga, yana saurin gajiya. A iya kuma ganin sa yana yawan tsuguno don hutawa in ya shiga wasan yara, ko kuma ya yi wani dan gudu kadan. Za a iya ganin sa yana yawan tari, ko samun kumburin ciki (musamman bangaren dama inda hanta take), ko kumburin kafafu, sa’annan ba ya girma kamar sauran yara.
Wasu iyayen a kauye a wannan lokaci ne suke samo wanzami ya yi wa yaro mai wannan alamu balli-balli a kirji, musamman idan an ga kirji na harbawa da sauri-sauri. Mu kuma mukan ba da shawarar kada a yi haka, a samu a kai mai wannan matsala ko dan karamin asibitin kauyen ne, wadanda su kuma za su tura su inda ya dace.
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo
Yawanci jariran da ake haifar su a asibiti suna da gatan cewa sai likitan yara ya duba su sarai kafin su tafi gida. To a irin wannan dube-duben ne likitan yara kan gano idan akwai wata matsala tattare da wannan jinjiri. Idan aka ga alamun ciwon zuciya to babu tafiya sai likita ya yi aune-aune da gwaje-gwaje an gano irin ciwon, kuma a dauki mataki cikin lokaci. Haka nan kuma wadannan shawarwari za su taimaka wajen rage yara masu ciwon zuciya:
1.    Yana da kyau mace mai ciki ta rika zuwa awo da zarar ta ga alamun ta samu juna biyu domin wasu ire-iren wannan ciwon na zuciya tun a ciki akan iya gano su ta hanyar na’urar daukar hotunan cikin. A wasu kasashen akan fada wa iyayen jariri halin da yake ciki tun jariri na ciki.
2.    A wurin awo kuma akan tantance magunguna da suka dace da mace mai ciki, ba wadanda za su kawo lahani ga dan da ke ciki ba. Don haka sayen wasu daban a bayan fage ba zai kawo da mai ido ba. Akwai irin wadanda ta wannan kafa muka ce za a iya nema kamar multibite, ko pregnacare mai kunshe da bitaman iri-iri da uwa da jariri kan bukata.
3.    Mace mai ciki kuma ta guji shan magungunan gargajiya, domin suna daya daga cikin abubuwan da sukan kawo wannan ciwo.
4.    Da zarar mai ciki ta ji wani zazzabi, ko mura, yana da kyau a je a ga likita wanda zai ba da maganin da ya dace.
5.    Kada mace mai ciki ta sha barasa ko taba sigari saboda lahaninsu ya fi yawa a kan jaririn da ke ciki.
6.    Mace mai ciwon suga mai juna biyu ita ma yana da kyau ta ranakun zuwa wurin likitanta ba fashi don a rika auna yawan siganta don kada ya yi wa jariri lahani.
7.    Hukumomi ko masu hannu da shuni su rika daukar nauyin yara wadanda aka samu da irin wadannan cutuka na nakasa, musamman ta hanyar kafa gidauniya da ba mu da su sosai a Arewa, wato irin na ‘Kanu Heart Foundation’, wadanda suke shiga lungu da sako da asibitoci domin gano masu irin wannan ciwo, yawanci a Kudu, ana tallafa musu domin yi musu aiki a zuciyar. Yanzu ci gaban kimiyya ya sa kusan duk irin ciwukan zuciya na yara, akan gyara su ta hanyar tiyata.
8.    Wadanda suke da wannan ciwo, amma likita ya ba su tabbacin ba wata damuwa da za ta same su idan suka bi ka’idojin da aka ba su, to za su iya rayuwa kamar kowa idan suka kwantar da hankalinsu.