✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA Hanyoyin Kariya Da Magance Matsalar Kwarkwata

Ba kamar kudin cizo da kwaron kazwa ba, su kwarin kwarkwata za su iya kama kowa, mai tsabta da maras tsabta, wanda gidansu akwai abin…

Ba kamar kudin cizo da kwaron kazwa ba, su kwarin kwarkwata za su iya kama kowa, mai tsabta da maras tsabta, wanda gidansu akwai abin hannu da wanda babu. Ita ce babbar matsalar da ta fi sa kaikayin kai ga yara ’yan mata, musamman ’yan makaranta, fiye ma da amosanin ka, a wasu lokutan ma har da manya mata. Maza da yake a yanzu zamani ya zo suna yawan aske kawunansu, an bar yin Ciko da Afro, abin ya yi sauki sosai a tsakaninsu. A kananan matan ma, masu gashi da yawa sun fi marasa suma saurin kamuwa.

kwarin sukan shiga kan yarinya ne daga wata mai ita zuwa maras ita, kamar a wurin wasa ko a zaman aji na makaranta ko ta musayar kallabi da dai sauran wuraren da yara mata kan iya haduwa su yi ma’amala. kwarin idan suka shiga kai jini suke zuka. Kusan a kididdiga, a duk yara mata goma sai an samu a kalla daya mai kwarkawata, wato a aji mai ’yan mata hamsin akan samu a kalla biyar masu matsalar, kuma ba wuya su sa wa na kusa da su.
Hanyoyin kariyar ke nan suna da wahala in dai har yarinya na zuwa makaranta inda za ta iya kwasowa ba ta sani ba. Don haka dole a lura da yarinya mai yawan susar kai, a rika wanke mata kai da maganin shamfo mai kashe kwayoyin a kyamis kamar maganin permethrin da ire-irensu, a dafa kallabi da ma riguna a ruwan zafi don kashe kwayayen. Wasu lokuta irin injin nan na busar da kai mai huro fankar zafi kan kashe su da kwayayensu. Idan abu ya yi sauki, a gargade ta da barin musayar kallabi da wasu a makaranta, kuma ta yi nesa-nesa da masu yawan susar kai, duk dai don kada a sake dauka.