✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LAFIYAR MATA DA YARA Amsoshin tambayoyi

Na ji amsar da ka ba wata a kan alamomin ciwon daji na mama. To ni wasu lokuta sai kan maman ya bushe ya rika…

Na ji amsar da ka ba wata a kan alamomin ciwon daji na mama. To ni wasu lokuta sai kan maman ya bushe ya rika tsagewa musamman ma bayan shayarwa. Ko shin wannan ma alamar ciwon ce?

Daga Hafsat A.

Amsa: A’a, wannan ba ya daya daga cikin alamun da aka zayyana. Wannan bushewar sandiyyar miyau da jaririn ya bari ne, shi ne kan sa hakan. Abin yi shi ne, duk lokacin da ya gama sha sai ki wanke ki dan shafa man shafawa kadan, kamar man basilin. Wannan zai hana miyau ya bushe ya tsattsaga miki kan mama.

 

Ko akwai wata tiyata ne da ake yi wa masu ciwon sikila?

Daga Atama Anthony, Nasarawa

Amsa: Tiyatar warkar da ciwon sikila mun sha fadarta a nan cewa tiyata ce ta dashen bargon kashi daga wani mai lafiya zuwa mai ciwon sikila. Amma idan kana nufin wane nau’in tiyata aka fi yi wa masu ciwon sikila, sai a ce maka an fi yi musu tiyatar kashi saboda yawan ciwon kashi da sukan samu, da ta cire matsarmama saboda yawan ciwon duwatsun matsarmama da sukan samu. Wadansu likitocin ma suna ba wa mata masu ciwon sikila wadanda suke da juna biyu suka zo haihuwa zabin tiyatar C.S ta cire yaron ba sai ta sha wahalar haihuwa ba.

 

Mai dakina ta haihu sai fatar cikin ta tattare, har da nankarwa. Shin me za ta rika yi domin su dawo kamar da?

Daga Aminu Lauya

Amsa: Wannan ai ko da ba ta yi komai ba lokaci zai zo da duka komai zai baje. Yana da alaka da ’yar kibar da mata kan kara lokacin da suke da juna biyu. Don haka da zarar kibar ta fara bajewa su ma alamomin fatar za su baje. Amma dai idan ana so abin ya tafi da wuri sai an hada da motsa jiki da shafa mai wanda aka yi musamman domin shafa wa nankarwa. Za a iya samun man a manyan shaguna ko kyamis.