✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Zabar Mijin Aure (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yanmatanci.…

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani kan ladubban dabi’un da suke bayyana lokacin ’yanmatanci. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.

Ladubban ’Yanmatanci
1.    Ladubban Kwalliya: Son yin kwalliya wata babbar dabi’a ce cikin dabi’un ’ya mace, shi ya sa ko yaran da ba su balaga ba suna son yin ado da kwalliya, don haka ne Allah SWT Bai haramta yin kwalliya da ado ba, sai dai ya yi umarnin a boye su daga ganin mazan da ba muharramai ba. Yana da matukar alfanu mace Musulma ta san irin kwalliyar da ta halatta da wacce ba ta halatta ba, kuma ta san irin kwalliyar da ya halatta ta bayyana da wacce ya zama tilas ta boye ta. ’Yar uwa Musulma ta sani cewa Allah SWT Ya umarci dukkan Musulmi mata da kada su bayyanar da adonsu face ga mazan da ba aure a tsakaninsu har abada, kamar yadda ya zo a cikin Aya ta 31 cikin Suratul Nur. Ga ladubban yin kwalliya kamar haka:
•    Yin Kwalliya da ado cikin salo mafi kyau, kuma mafi dacewa ya halatta; sannan ayyanar da ita ga ’yan uwa mata da mazan da babu aure a tsakani har abada; ko mazan da ba su da sha’awa, ko yara kanana, shi ma ya halatta;
•    Bayyana kwalliya ga dukkan namijin da ba muharrami ba haramun ne, kamar yadda ya zo a cikin wannan Ayar da na ambata a sama. Haka bayyana kwalliya ga mazan da ba muharramai ba, ta hanyar sanya abubuwa masu fitar da sauti in jiki ya motsa kamar awarwaro, sarkar kafa, ko ta hanyar takalmi mai fitar da sauti in ana tafiya, shi ma yin hakan bai halatta ba. Don haka rufe jiki da hijabi bai bada damar sanya irin wadannan kayan kawa masu fitar da sauti matukar mace ta san za ta bayyana gaban mazan da ba muharramanta ba.
•    Caba ado a fuska, ta hanyar shafa hoda mai canza launin fata, ko ta hanyar rina lebba da jan-baki mai launin bau! Shafa man lebe mai kyalkyali; yin fenti a fatar saman ido, jan girar ido da jagira har ta wuce asalin inda tsawonta ya tsaya, da sauran ire-iren wadannan kwalliya na adon fuska, haramun ne mace Musulma ta bayyanar da su ga mazan da ba muharramanta ba.
Wasu daga ire-iren wadannan kwalliya ma bai dace da mace mai mutunci ta yi su ba; domin maimakon su fito da kyawun fuskar, wasu sai dai su sanya mata launin fitsara da kekashewar zuciya; wasu kuma irin adon mutanen da ba Musulunci a zuciyarsu ne, wanda haramun ne kwaikwayon dabi’u irin nasu.
Don haka caba ado kaca-kaca a fuska bai dace da mace Musulma ba, sai dai in za ta rika rufe fuskarta ne a kodayaushe ta caba irin wannan adon. Amma yin ado sassauka, da kayan kwalliya masu saukin rini, ta yadda za su inganta kyawun fuska ba tare da sun canza wani abu daga gare ta ba shi ne ya dace da kowace Musulma.  
•    Sanya turare mai kamshi sosai, irin wanda duk inda mace ta wuce sai an ji kamshinsa, yin hakan bai halatta ba, sai dai mace ta sa turare mai sanyin kamshi ta yadda ita kadai ke jin abinta, sai kuma wanda ya matso kusa da ita sosai.
•    Amfani da man shafawa mai kamshi sosai, ko mai canza launin fatar jiki, ko mai haifar da wata tangarda ga fatar jiki; shi ma bai halatta ba.
2.    Ladubban Sanya Tufafi: Kamar yadda ya gabata, mace Musulma za ta rufe jikinta gaba daya da hijabi kodayaushe idan bukatar bayyana gaban mazan da ba muharramai ba ta kama ta; kamar yadda Allah SWT Ya yi Umarni a Aya ta 59, cikin Suratul Ahzab:
“Ya Kai Annabi! Ka cewa Matanka da ’ya’yanka da matan Mu’uminai su kusantar kasa daga manyan tufafin da ke kansu. Wancan ya fi sauki da a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai Gafara Mai Jinkai.”
Wannan Aya mai albarka ta bayyana mana cewa wannan umarni na Allah SWT, ya shafi dukkan matan Musulmi: masu aure, zawarawa, masu takaba da ’yan mata. Don haka babban kuskure ne a ketare iyakokin Ubangiji, ta hanyar shigar da ke nuna kawa da bayyana siffofin jiki da yawancin ’yan matan wannan zamanin suke yi da sunan ’yan matanci ko da sunan tallata kai don a samu mijin aure. Manzon Allah SAW Ya bayyana irin wadannan mata da cewa su tsinannu ne, don haka in an gan su a tsine musu, kuma Ya ce ba za su ji kamshin aljanna ba, ballantana su shige ta. Don haka yake ’yar uwa ki sani, duk wani farin jini, duk wani arziki, duk wani matsayi da daukakar da za ki samu a dalilin yin shigar da ta saba addininki, za ki ji dadinsu ne na dan kankanin lokaci kadai, azabar lahira kuwa madauwamiya ce; don haka kar ki bari shaidan ya yi amfani da zafin kan ’yanmatanci ya halakar da ke, ya hana ki dacewa da aljanna, ya tabbatar miki kasancewa cikin azaba; in kunne ya ji, jiki ya tsira!
3.    Ladubban Yanga da Yatsina: Zafin kai irin na ’yanmatanci nasa har macen da ba ta da dabi’un yatsina, yanga da kwarkwarsa ta ji tana son yin wadannan dabi’un a wasu lokuta. Wadannan dabi’u suna shagaltar da da namiji wata sa’in ma har su tsunduma shi cikin sha’awa. Haramun ne ’yan mata su rika yin wannan dabi’u ga samarinsu, ko ga mazan da ba muharramansu ba.
Wadannan dabi’u sun halatta ne kadai mace ta yi su ga mijinta. Wadannan sun hada da: salon magana da tsara kalami cikin irin siga mai jan hankali, kashewa ko sanyaya murya wajen magana; yin wani furuci marar ma’ana, illa ma’anar saka fitina a zuciyar mai saurare; yin fari da ido, harara irin ta wasa, kallon hadarin kaji cikin tsiwa; gatsine da murguda baki cikin salon jan hankali; salon murmushi daban-daban cikin siga mai kayatarwa, salon tafiya da murgude-murgude; warwatsa hannaye cikin yanga; da sauran ire-iren wadannan dabi’u duk haramun ne mace mai jiran aure ta yi su ga wani mutum wanda ba muharraminta ba. Sai dai wacce yana daga cikin ainihin dabi’arta yin daya daga dikin wadannan dabi’u; to ita ma sai ta sa kulawa sosai wajen yadda take mu’amula da mazan da ba muharramanta ba, don tsaron mutuncinta da imaninta.