✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Zabar Mijin Aure

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan ladubban da mace Musulma za ta yi amfani da su wajen zabar mijin aure. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, kuma ya amfanar da su, amin.

Ladubban Jiran Fitowar Miji Mafi Dacewa:

Ladabi Na 1: Kyakkyawan kudiri: kulla niyyar lokacin yin aure ga ’ya mace ya fi ta’allaka ne ga iyayenta, domin su za su kulla niyyar aurar da ita a lokaci mafi dacewa gare su, ko a lokacin bayyanar miji mafi dacewa ga ’yarsu. Duk da haka yana da kyau ga wacce ta mallaki hankalin kanta, ta kulla kyakkyawar niyya a zuciyarta game da aure, domin aure ibada ne gare ta, kamar yadda yake ibada ga namiji. Don haka sai mace Musulma ta kulla niyyar ayyukan alheri da suka dangaci aure, kamar bin ka’dojin addini, dukkansu yayin da take zaman jiran fitowar mji mafi dacewa gare ta, kamun kai da hakuri da yin ladabi ga iyaye da magabata, kudirin yin zaman aure domin Allah da fatan samun kyakkyawan sakamako, da sauran kyawawan kudirori da suka dace da yanayi da kuma lokaci.
Ladabi na Biyu: Tsananta Addu’a
Sai mace Musulma da take a halin jiran fitowar mijin aure ta kasance mai tsananta addu’a da kara dagewa wajen tsayar da addininta, da yin abubuwan karuwar imani a zuciya, kamar su yawan yin azumin nafila a-kai-a-kai, sallolin nafila a sulusin karshe na dare, yawan yin sadaka, karin kyautatawa ga iyaye da ’yan uwa makusanta da makwabta. Yawan yin sallar neman zabin Allah (watau Sallar Istikhara); dagewa wajen guje wa aikata ayyukan sabon Allah, musamman kanana irin wadanda aka raina; guje wa cin haram; yawan yin tasbihi da istigifari da raya zuciya da yawan tunanin Allah Madaukakin Sarki da Yawan gode masa.
Ladabi Na Uku: Biyayya Ga Dokokin Allah:
Wajibi ne ga mace Musulma, mai tsoron Allah ta kiyaye dokokin addini gaba dayansu lokacin da take zaman jiran fitowar mafi dacewar miji gare ta. Wannan kuwa su ne kasancewa cikin cikakkiyar hijabi duk lokacin da za ta fita waje, da kame kanta daga sakin jiki ga mazan da ba muharramanta ba; ta san cewa bai halatta aikata duk wasu ayyukan da za su ja ra’ayin maza zuwa gare ta, kamar fita cikin shiga irin wacce ta saba wa addini, caba kwalliya da bayyanar da ita a kodayaushe. Haka kuma haramun ne tsayawa da samari a rika hira a kofar gida ko a cikin mota. Ki sani, yake ’yar uwa mai karamci, Allah Ubangiji Ya sanya wasu dokoki gare ki, ba don takura miki ba, a’a, sai don Ya karrama ki, Ya daga darajarki, kuma Ya tabbatar maki da mutuncinki; don haka ba daidai ba ne ki wulakanta kanki, ta hanyar juya baya ga wadannan dokoki na Allah Madaukakin Sarki, ki rika shiga irin shigar fajiran mata, don dai kawai ki jawo ra’ayin maza su ce suna sonki; wannan ba shi zai jawo miki farin jini ba, babu irin abin da ke jawo wa ’ya mace farin jinni kamar tsoron Allah. Ba a samun tsoron Allah kuwa sai in an yin ladabi ga dokokinSa sau da kafa.
Ladabi Na 4: Riko da Addini: Idan har kina da burin samun miji mai inganci, wanda zai tsare miki dukkan hakkokinki na aure, to ki kasance mai riko da addininki komai dadi komai tsanani, ki sani, mace mai riko da addini ita ce mafi tsadar mace a wannan zamani namu, domin ita ce wacce Fiyayyen Halittun Allah kuma Manzon Allah SAW Ya yi wa tambarin cewa ita kadai ya halatta a nema da aure, ga shi muna cikin wani irin zamani da riko da addini ya zama wani abu mai wuyar samu a cikin al’umma. Don haka ba ki da wani abu mafi tsada kuma mafi muhimmanci gare ki a lokacin jiran miji kamar riko da addini. Kuma ki sani, riko da addini ya wuce sanya zumbulelen hijabi da tara ilimin addini, tabbas wadannan dabi’u ne masu kyau kuma abin yabawa, amma riko da addini ba iyakarsa ke nan ba, ya kunshi dagewa wajen yin ayyukan ibada da kauce wa haramtattun abubuwa da yawan yin abubuwan raya imani cikin zuciya, ta yadda da imaninki ya ragu za ki farga ki yi kokarin gyara dabi’unki na Islama don samun karuwar imani cikin zuciya.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.