✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ladubban Sulhunta Ma’aurata

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su…

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan hanyoyin sulhunta ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.

Gyara:
Assalamu Alaikum. Matakin sulhun da kika sawa suna ‘fitina’ bayaninsa da kika bayar a filinki na DUNIYAR MA’AURATA na 1/1/16 ya fi dacewa da ‘kissa’ don fitina tashin hankali kenan.

Amsa: Abubuwan da Allah Ya rahamta ‘ya mace da su na ruxar da xa namiji suna da yawa sun fi karfin a kirasu da kissa kaxai. Bayan haka kuma Annabi Sallallahu Alayhi wa Sallam ne Ya faxi cewa “Ban bar wata fitina a bayan kasa ga al’ummata da ta wuce fitinar ‘ya mace” to ai ba ita macen ce fitina ba sai dai abubuwan da take yi da hanyoyin da take bi na ruxar da hankalin xa namiji su ne fitinar. Da fatan Allah Ya sa mu dace amin.

Mataki na Farko: Idan abubuwa suka rincabe tsakanin ma’aurata, ta yadda husuma ta ki kare wa a tsakaninsu, kuma sun yi zaman neman mafita tsakaninsu ko tare da wasu daga cikin magabatansu ko aminansu, amma duk da haka sulhu ya ki samuwa. To sai ma’aurata su aikatar da wannan umarni na Allah Maxaukakin Sarki da ke cikin Aya ta 35, Suratun Nisa’i:
“Kuma idan kun ji tsoron sabawar tsakaninsu, to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu…”
Sharaxi:
Mu lura cewa akwai sharaxin cewa sai abubuwa sun rincebe sosai har ana tsoron samun sabuwa mai tsanani sosai ko kuma ana tsoron mutuwar auren a dalilin wannan husuma sannan ne za a nemi yin zaman sulhun da wannan Aya take magana akai. Don haka ba kowace karamar husuma ba ce za a ce bari a aiwatar da wannan Aya mai Albarka.
Wannan umarni ya faxa akan bangarori 4:
1. Su ma’auratan su amince da kansu cewar za su tsayar da waxanda za su yi masu alkalanci domin daidaitawa da samar da zaman lafiya tsakaninsu.
2. Magabatan ma’aurata su ma suna iya tsaida maganar cewa ya kamata a samar da masu sulhu da za su zauna su yi alkalanci tsakanin ma’aurata don kawo karshen husumar da ke tsakaninsu.
3. Shugaba na Musulunci, kamar maigari, mai unguwa ko limamin Masallaci, in an kawo karar Husumar aure gabanshi sai ya nemi ma’auratan su gabatar da amintattu daga mutanensu don su zauna suyi alkalanci tsakaninsu.
4. Alkali na kotun Musulunci, da husumar Maaurata ta iso gabanshi,  wannan shine abinda zai aikata ba wai ya wuce ya zartas da hukunci da kanshi ba, shi kadai ba. Haka nan in karar husuma auratayya ta faxo gaban ‘yan sanda ko wasu mahukunta daban, wannan umarni na Allah Maxaukakin Sarki shine za ayi aikin sulhunta Ma’aurata da shi wasu dokoki daban na bil’adam ba.
Rashin yin aiki da wannan Umarni na Allah Maxaukakin Sarki babban kuskurene da ma’aurata, magabatansu da kuma mahukunta na kasa suke tafkawa, kuma wannan kuskure ya riga ya zama ruwan dare ya yi katutu cikin yanayin zamantakewar auratayya a kasar Hausa. Rashin bin wannan umarni na Allah Maxaukakin Sarki babban haxarine kwarai da gaske. Kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya gargaxemu cikin littafinsa Mai Tsarki, Aya ta 45; Surah ta 5:”…Kuma wanda bai yi hukunci ba da abinda Allah Ya saukar ba to waxannan sune azzalumai.”
Don haka ko don mu fitar da kanmu daga waxanda ake zargi da zalunci sai mu yaki zuciyarmu, kuma mu yaki shayxan mu rika aiki da wannan umarni na Allah Maxaukakin Sarki a lokacin kokarin kwantar da husuma tsakanin ma’aurata.
Zabar Masu Alkalanci: Duk xaya daga cikin waxancan bangarori na sama da umarnin can na Allah Ya faxa kansa a yayin da husuma ta tsananta, to shi ne zai binciko, ko ya umarci ma’auratan su zabo wanda zai yi masu alkalancin daga cikin ‘yan uwansu waxanda suka cika waxannan siffofin:
Masu tsananin riko da taka tsan-tsan da addininsu; maza balagaggu, masu cikakke kuma tsarkakken hankali; sannan masu ilmin addini da na zamantakewa da kuma ilmin hakkokin auratayya da sanin hanyoyin raba ko sulhunta ma’aurata; masu rikon amana waxanda za su yi domin Allah kuma daga kowane bangare na ‘yan uwan ma’auratan.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.