✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘labarin tarin tsintsiya’

Barka da warhaka Manyan Gobe Assalamu alaikum Manyan Gobe, tare da fatan kuna lafiya. Yau na kawo muku labarin ‘tarin tsintsiya’. Labarin na kunshe da…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Assalamu alaikum Manyan Gobe, tare da fatan kuna lafiya. Yau na kawo muku labarin ‘tarin tsintsiya’. Labarin na kunshe da yadda sarkin yawa ya fi sarkin karfi. A sha karatu lafiya.
Taku,Gwaggo Amina Abdullahi

‘labarin tarin tsintsiya’

Akwai wani dattijo, yana da ’ya’ya da yawa, kuma yana da dimbin arziki. Akwai abu daya da ke damunsa. Abin shi ne rashin hadin kan ’ya’yansa, har ta kai ga kullum suna cikin fada da juna. Shi kuwa yana tsoron barinsu a hakan. Domin yana ganin cewa za su iya kashe junansu domin gadon da zai bar musu.
Ranan ya kwanta jinya. Sai ya dauki tsinken tsintsiya daya ya bai wa babban dansa. Ya ce da shi ya karya. Ganin hakan sai abin ya bai wa dan sa dariya. Ya karya ba tare da wata gajiya ba.
Sai ya dauko tarin tsintsiya a kulle. Ya ce da dansa ya karya. Sai dan yayi ya karya, amma ya gagara. Sai ya ce da ‘ya’yansa idan kuka hada kanku babu wanda zai shiga tsakaninku.
Daga nan sai yaran suka yafe wa juna. Suka hada kansu.
Da fatan Manyan Gobe za su tsaya wa dan uwansu a kodayaushe domin yin hakan na hana makiyi cin nasara akansu.