Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Edward Egbuka, ya karyata labarin da ake yadawa cewa an sace ’yan sanda 10 yayin da suke dawowa daga a aikin samar da tsaro a zaben Gwamnan Jihar Osun.
Da yake karyata labarin a ranar Laraba, ya bayayana ’yan bindiga sun kai wa ayarin ’yan sandan hari ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, amma ba su yi garkuwa da su ba kamar yadda ake yadawa.
- Malamin Lissafi ya yi wa dalibarsa illa a kashin baya da bulala
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Annobar Kwalara Ta Ki Ci Ta Ki Cinyewa A Kano
Kwamishinan ya kara da cewa a lokacin da aka kai wa ’yan sandan hari, dukkansu sun tsere cikin daji domin gudun kada a yi garkuwa da su.
Egbuka ya ce a lokacin da kura ta lafa, dukkan jami’an su 10 da ake zargin an yi garkuwa da su sun dawo cikin koshin lafiya daga maboyarsu, inda a karshe suka koma tare da abokan aikinsu jihar Nasarawa.
A ranar Lahadi ce Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Nasarawa ta bayar da rahoton cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan sanda 10 a hanyarsu ta dawowa daga aikin zaben gwaman Osun da aka kammala a satin da ya wuce.
Wata majiyar ’yan sanda ta ce lamarin ya faru ne a Obajana, a Jihar Kogi, a ranar Lahadi.