✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Labarin Hashidu dan kasuwa

Barka da warhakaManyan Gobe Yaya karatu? Da fatan kuna bibiyar karatu sau da kafa.  A wannan makon Kawunku Naseeru ya taho muku da guzurin labarin…

Barka da warhaka
Manyan Gobe

Yaya karatu? Da fatan kuna bibiyar karatu sau da kafa.  A wannan makon Kawunku Naseeru ya taho muku da guzurin labarin wani bawan Allah mai suna Hashidu. Ina fata za ku bi labarin don tsintar darussan da yake koyarwa. A sha karatu lafiya. Naku: Kawu Bashir Musa Liman

Labarin Hashidu
dan kasuwa

Daga Naseeru Taneemu Annuree

A wani zamani mai tsawo an yi wani bawan Allah mai tausayi da taimakon na kasa da shi da ake kira Hashidu. Allah Ya azurta shi, ya kuma samu daukaka a harkokin kasuwancinsa. Domin duk lokacin da ya fita cin kasuwa garuruwa, yana dawowa da gagarumar riba fiye da duk wani dan kasuwa a garinsu. Kusan kowa a garinsu yana kaunarsa, saboda mutum ne da bai dauki abin duniya da zafi ba. Kusan duk ribar da ya samu tana karewa wajen taimakon talakawa ne. Wannan ya sa kullum yake shan yabo daga takalawa, a lokaci guda kuma yana fuskantar hassada daga wasu abokan kasuwancinsa.
Wata rana a kan hanyarsa ta dawowa gida daga harkar kasuwancinsa, sai ya hadu da ‘yan fashi a hanya. A nan suka kwace duk kudadensa. Suka kuma lakada masa duka. A karshe suka sare masa hannayensa da kafafuwansa. Sannan gudu suka bar shi a wajen.
A ka ci sa’a wasu daga cikin mutanen garinsu suna dawowa a hanya suka tarar da shi yana jan gindi. A nan suka dauke shi suka nufi gida. Bayan sun isa gida, sai aka fara masa jinya har ya warke. A karshe ya koma talaka, amma duk da haka kamar kullum mutane suna samunsa cikin fara’ar da ya saba, bai nuna alamar damuwa da abin da ya same shi ba, inda ya ce musu Allah ne ya kaddara faruwar hakan a gare shi.
Mafi yawan mutane a tunaninsu kullum za su same shi cikin bakin ciki ne, saboda ko fita kofar gida ba ya iya fita.
Wata rana wadansu mutane suka same shi, suka tambaye shi me ya sa kullum yana cikin fara’a ba tare da la’akari da asarar da ta same shi ba? Ko da jin haka, sai Hashidu ya yi murmushi, sannan ya ce musu, shi bai yi asarar komai ba. Cikin mamaki suka tambaye shi kamar yaya? Sai ya ce “Ban yi asarar zuciyata ba. Da ita nake bauta wa Allah ba da hannu, kafafu ko dukiya ba. Saboda haka duk wanda ya rasa zuciyarsa ga shaidan shi ne, wanda ya yi asara duniya da lahira.”