Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan fili namu na Manyan Gobe. Tare da fatan an koma karatu bayan an sha dogon hutu. A yau na kawo muku labarin Hamsatu mai hakuri. Labarin na kunshe da yadda hakuri ke janyo ci gaba. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi
An yi wata mummunar ambaliya a wani kauye. Sakamakon hakan, sai yunwa ta kama garin. An rasa abinci a kauyen. Mutanen kauyen sun wahala sosai.
Ba a samun abinci a ko’ina sai a gidan wani attajiri. Kullum sai an yi dogon layi a gaban gidansa domin karbar abinci. Mutane sukan yi hayaniya kafin su samu rabonsu.
Hamsatu kullum ita ce a karshe da hakan ya sa ba ta samun isasshen abinci, don sai wanda ya rage ne ake ba ta.
Kamar kullum, washegari sai Hamsatu ta sake zama ta karshe, inda da kyar ta samu guntun burodi. Tana gutsurar buredin sai ta tsinci kudi a ciki. Sai ta mayar wa attajirin kudinsa. Abin ya ba shi mamaki kwarai da gaske. Ganin irin yanayin da ake ciki amma ta mayar masa da kudin.
Sai attajirin ya ce ya bar mata kudin hasali ma ya kara mata da wasu kudin masu yawa. Sannan ya umarci masu raba abincin su rika farawa da Hamsatu kuma su tabbatar suna ba ta isasshen abinci.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a wannan labari kamar yadda masu iya magana kan ce “Mahakurci, mawadaci.”