Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.
Anty Nabilah na karanta labarin wacce aka aura ma mijin da ba ya haihuwa. Ni ma nawa labarin ya yi kama da nata. Ni Babana ne ya yi mani auren dole da dan babban abokinsa wanda ya ninka ni a shekaru.
Abokin nasa wanda ya riga mu gidan gaskiya ya bar wasiyyar cewa in na isa aure ya hada ni da daya daga cikin ’ya’yansa.
Shi kuma Baba sai ya hada ni da babban cikinsu domin shi kadai ne mai abin kansa a lokacin.
Ina da shekara daya a gidan ban samu ciki ba danginsa suka taso ni gaba da zagi da wulakanci da cin fuska.
Wata rana da suka same ni har gida suna zazzaga min ruwan wulakanci, na kasa daurewa na mayar masu, suka same ni suka lakada min duka, suka farfasa min jiki.
Na je gidanmu babana ya koro ni ya ce in je in zauna in yi ta hakuri kuma ko me za su ce min nan gaba kada in kara mayar masu da magana.
Bayan kamar wata bakwai kuma suka kara sauke min wani kwandon rashin mutuncin, na yi shiru ban ce da su uffan ba, hakan shi ma ya zama laifi, suka ce suna min magana na yi banza na kyale su ina masu kallon banza.
Nan ma suka kara lakada min duka har da karya min hannu.
Na je gidanmu, nan ma mahaifina sai dai ya kira mai dori aka dora ni ya ce in koma gidan aurena.
Mahaifiyata ta ce “Haba Malam! Don Allah ka bar ta sai ta samu lafiya mana?”
Ya ce in ta kara sa baki a bakin aurenta. Haka na koma na ci gaba da kwasar wulakanci daga wurin mijina da danginsa.
Mijina ba maganar kirki a tsakanina da shi, ko kirana zai yi sai dai ya ce ke bakarariyar nan?
Kuma ya rika cewa duk wata mace in ba Bafullatana ba ce ba ta cika mace ba.
Kullum yana kwatanta ni da matarsa ta farko wacce ta rasu wajen haihuwar ’yarsa wacce shekarunta goma lokacin da ya aure ni.
Ko tuwo na yi sai ya ce nata ya fi dadi. In fura na dama masa sai ya yi mitar cewa ta fi ni iya damu.
Haka ma wajen ibadar aure da komai da komai na rayuwar aure.
Duk ranar da na kuskura na mayar masu da magana kuwa ranar ya kwabde ni ya tafi ya bar ni da ciwon jiki.
Akwai ranar da ya taka min ruwan ciki da kafarsa ya ce cikin nawa bai da wani amfani tunda ya kasa daukar ciki.
Har sai da na shekara tara a cikin wannan rayuwar kunci. Sai da labarin halin da nake ciki ya isa kunnen kanin mahaifina da ke zaune a kasar waje lokacin da ya zo ganin gida.
Baffa Aliyu shi ne ya kwatar min ’yancina ya kai mijina kotu ya nemi a raba auren.
Suka ce sai an biya su duk abin da suka kashe lokacin aure da duk abincin da suka ciyar da ni tun ranar farko har zuwa yau.
Baffana ya amince ya biya su duka aka ba ni takardata. Don a tura min haushi a cikin wata daya danginsa suka nemo masa budurwa da bazawara sakin wawa suka aura masa.
Ni ma kuma ina gama idda tsohon saurayina wanda na so in aura Baba ya hana, ya fito aka daura mana aure ya tafi da ni Kudancin kasar nan.
Wata tara cif na haifi da namiji. Shi kuwa tsohon mijina duka mata biyun har yanzu ba wacce ta haihu.
Amma duk da haka ban tsira ba wajen danginsa. Cewa suke ni da Baffana muka yi masa asiri matansa suka kasa haihuwa.
Wai baiwar haihuwarsa ce muka kwace da sihiri ta dawo wurina. Maimakon su fahimci cewa dan uwansu yana da matsala su nema masa magani.
Malama Nabilah na kawo labarina ne don ki taya ni yin magiya ga iyaye su daina yi wa ’ya’yansu auren dole, kuma su rika kwatar wa ’ya’yansu mata ’yanci in ana cin zalinsu a gidan aurensu.
Ni dai ina girmama mahaifina ina yi masa ladabi da biyayya, amma wallahi ba na jin soyayyarsa ko kewarsa a zuciyata, saboda na kasa yafe masa a kan wahalar da ya tursasa ni a ciki a dalilin aure.
Na yi masa ladabi na auri wanda ba na so, amma da aka zo ana cutar da ni na so a ce Babana ya kwato ni daga wannan ukuba.
Don haka a zuciyata, soyayyar mahaifina ta koma ga Baffana, domin shi ya fid da ni daga cikin ukuba, ya ba ni ’yanci irin wanda Allah Ya ba dukkan wani bil Adama. Don haka shi ya cancanci kauna a zuciyata.