✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kyautar $10,000: Matashiyar da ta lashe kyautar Daily Trust ta 2020

An ci zarafinta an mata aure dole tana shekara 14, ta yi takaba tana shekara 21

Wata matashiyar lauya ’yar kasar Gambia, Musu Bakoto Sawo ta lashe Kyautar ’Yar Afirka ta shekarar 2020.

Musu Bakoto Sawo, malamar jami’a ce, kuma mai rajin kare hakkin mata da yara da kuma kawo sauyi ce tun tana shekara tara a duniya.

Bayan an yi mata kaciyar mata, an yi mata auren dole tana da shekara 14, sannan ta shiga takaba tana shekara 21, yanayin da ta yi amfani da shi wurin yakar wadannan abubuwan.

Ta zama gwarzuwar gasar ce bayan alkalan kwamitin gasar karkashin tsohon Shugaban Kasar Botswana, Festus Mogae, sun bi diddigin bayanan dukkanin ’yan takarar.

Kwamitin gasar ta nahiyar Afirka wanda ya tattaro mamboninsa ne daga yankunan nahiyar, ya fara zaman tantance ’yan takarar ne a ranar 10 ga watan Disamba, 2020 sannan ya sanar da sunan gwarzuwar a ranar 4 ga Janiarun 2021.

’Yan kwamitin sun hada da Mis Mona Omar (Arewacin Afirka), Mis Gwen Lister (Kudancin Africa), Mista Amadou Mahtar Ba (Yammacin Afirka), Fasto Rigobert Minani Bihuzo (Tsakiyar Afirka), da Malam Kabiru Yusuf (Yammacin Afirka).

‘Ta cancanta’

Da yake jawabi kan tsarin tantance ’yan takarar, Doktar Mogae ya ce, “Musu Bakoto ta cancanti kyautar saboda dorewarta wajen neman kawo karshen cin zarain mata da yara ciki har da auren dole da kuma kaciyar mata”.

A shekarar 2008 ce aka fara bayar da Kyautar Dan Afirka na Shekara na kamfanin Media Trust Limited, masu buga jaridun Daily Trust, Aminya, Daily Trust on SaturdayDaily Trust on SundayTeen Trust da Kilimanjaro.

Media Trust wanda daya ne daga cikin jagororin kamfanonin jarida a Najeriya, ya kirkiro da kyautar ce da nufin wanzar da hadin kai, cigaba da kuma karrama ’yan Afirka da suka zama bin koyi ta wasu muhimman abubuwa da suka yi a bangarorin rayuwa daban-daban.

Mukaddashin Shugaban Kamfanin Media Trust, Nura Daura, a cikin wata sanarwa ya ce Kwamitin ya zabi lauyar ce saboda dorewarta wajen neman karshen cin zarafin mata da kananan yara mata, auren dole da kuma kaciyar mata.

Ya ce matar ta yi amfani da kwarewarta wurin ba da horo, bincike kulla dangantak da kuma bullo da shirye-shirye kare hakkin dan Adam a matakin al’umma, kasa da nahiyar da ma duniya baki daya.

Nura Daura ya ce muhimmancin Sawo a lokacin COVID-19 na da girman gaske, “inda abin ya fi yi wa mata illa, musamman a lokacin dokar kulle da mazaje suka rasa ayyukansu, wanda hakan ya haifar wasu matsaloli cikin har da gallazawa a cikin gidaje”.

‘Ta cancanci yabo’

Ya ce ta dauki gabarar kare hakkokin mata a fadin Afirka, wadda nahice da ta yarda da gargajiya, saboda haka ta cancanci kyautar.

Misis Sawo, lauyar kare hakkin dan Adam ce ta duniya kuma malama a Tsangayar Koyar da Aikin Lauya ta Jami’ar Gambia.

Ita ce kuma Shugabar Kungiyar Think Young Women mai kare hakkkin mata da kananan ’yan mata.

A shekarar 2017 sa samu kyautar Vero Chirwa daga Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam na Jami’ar Pretoria ta Kasar Afirka ta Kudu.

Tana kuma da cikin matasa 100 masu fada a ji a Yammacin Afirka na Gamayyar Matasan Yammacin Afirka a 20218.

A 2018 an ba ta kyautar ’Yan Kasar Gambia mai Ba da Kwarin Gwiwa.

Likita dan kasar Congo, Dokta Denis Mukwege, shi ne wanda ya fara karbar Dan Afirka na Shekara na Daily Trust a 2008.

Bayan shekara 10 da samun kyautar ta Daily Trust, Dokta Mukwege ya samu Kyautar Nobel ta Zaman Lafiya a 2018, saboda ayyukansa na jinyar matan da aka ci zarafi ko aka yi musu fyade a kasar mai fama da yaki.

Baya ga karramawar a matsayin ’Yar Afirkar ta Shekara ta Daily Trust na 2020, akwai kuma kyautar kudi Dala 10,000 da ta samu.