Mujallar Forbes mai bibiyar masu arziki a duniya, ta ce attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya faɗo daga matsayi na farko a jerin masu kuɗin nahiyyar Afirka.
Forbes ta ce a yanzu an samu wani dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert da ya sha gaban Dangote a matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka.
- Dan daba ya kashe limami saboda hana shi shan wiwi a Kano
- Jadon Sancho zai koma zaman aro a Dortmund
Sabon jerin attajiran da suka fi arziki a duniya da mujallar Forbes ta fitar ya nuna cewa Dangote ya sauko daga matsayin ne bayan dala biliyan $3.8bn ta ragu daga cikin arzikinsa.
Mujallar ta ce arzikin Dangote ya koma dala biliyan $9.7 a watan Janairun shekarar 2024, yayin da arzikin Johann Rupert dan kasar Afirka ta Kudu ya koma dala biliyan 10 a cikin watan Janairun shekarar 2024.
Duk da cewar shi ma attajirin Afirka ta Kudun ya rasa dala miliyan $700m cikin arzikin nasa, shi ne ya fi arziki a nahiyar Afirka, in ji mujallar ta Forbes.
Johann Rupert mai shekara 73 dai shi ne shugaban kamfanin kayan alatu na Compagnie Fiannciere Richemonte da ke kasar Switzerland.
Sai dai kuma har yanzu dai Dangote ne yake kan gaba a cikin jerin attaijirai da suka fi kudi a Afirka a jerin attajirai na jaridar Bloomberg da kudi dala biliyan $15.4bn yayin da Johann Rupert ke biye da shi da kudi dala biliyan $12bn.
Kazalika Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, ya koma attajiri na shida da ya fi kudi a Afirka daga matsayi na hudu da yake kai a baya, in ji mujallar Forbes.
Shi kuma Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, ya koma na 10 daga matsayi na shida a jerin attajiran da suka fi kudi a Afirka, a cewar Forbes.
Ana ganin faduwar darajar kudin Naira ta Najeriya da darajar kudin Rand na Afirka ta Kudu ya taka rawa wajen rage yawan arzikin attajiran na Afirka a rahoton mujallar Forbes.