Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana Najeriya a matsayin kasa da ta yi zarra a yawan matalauta a nahiyar Afirka, da mutum akalla miliyan 100.
Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Mista Mitthias Schmale ne ya bayyana hakan a yayin gabatar da rahotun Tattalin Arziki na Afirka na wannan shekarar (ERA 2023).
Rahoton ya bayyana Annoban COVID-19 da yakin tsakanin Rasha da Ukraine a matsayin wasu daga cikin manyan dalilai da suka janyo munanan matsalar talauci Afirka.
Kasashe da ke biye da Najeriya a yawan matalauta, a cewar rahoton sun hada da Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo da ke da matalauta mutum miliyan 67, sai Tanzaniya da mutum miliyan 36, sai kuma Habasha mai mutum miliyan 33.
- DAGA LARABA: Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai
- An kashe mai tsaron lafiyar alkali an sace ta
Babban jami’in na U.N wanda msanin tattalin arzikin kasa NOnso Obikili ya wakilta, ya shawarci gwamnatocin kasashen su samar da tsarin shugabanci na gari tare da karfafa habakan masana’antu a matsayin babban tsani na shawo kan matsalar.
A jawabin da ya gabatar, mashawarcin shugaban kasa a kan tattalin arziki, Dokta Tope Fasua ya ce ’yan Najeriya na rayuwa cikin tsarin rashin daidaito inda ake da wagegen giɓi atsakanin mawadata da matalauta.
Daraktan harkokin tattalin arziki da mulki a Hukumar Kula da Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Majalisar Dinkin Duniya (UNECA) Adam Elhiraika ya ce cigaban tattalin arzikin Nahiyar yawanci ya dogara ne kan fitar da abubuwan da ake sarrafawa a masana’antun manyan kasashen duniya.
Sai dai kuma hakan ya fuskanci tasgaro a dalilin a lokacin COVID-19 da kuma yakin da ake fama da shi a tsakanin Rasha da kuma Ukraine a yanzu.
Ya ce akwai bukatar kasashen Afirkan su inganta tsarin gudanar da masana’antunsu ta hanyar inganta fasaharsu a bangarori daban-daban.