✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kyankyaso: Kwaron da ke iya rayuwa tsawon mako daya babu kai

Suna kuma iya shafe wata daya ba abinci ko ruwa

Kyankyasai na daga cikin kwarin da ake gani a gidaje ba tare da gayyata ba. Kwaro ne mai fuffuke da kafafu kuma mai launin ruwan makuba.

A cewar masana, ana da nau’ukan kyankyasai kimanin 5,000 a duniya amma kadan daga ciki ake iya gani a sarari.

Wani abin mamaki game da rayuwar wannan kwaro kyankyaso shi ne cewa, yana iya rayuwa na tsawon mako daya bayan an datse kansa.

Dalilin haka inji masana shi ne, kyankyasai ba su bukatar baki ko hanci wajen numfashi. Suna da wata baiwa ta yin numfashi ta hanyar wasu kananan kafafe da ke jikinsu.

Kazalika, kyankyasai na iya shafe wata daya ba tare da abinci ko ruwa ba.

Kwari ne masu zafin nama a wajen tafiya. Zafin naman nasu shi ke zama a matsayin hanya daya da suke tseratar da ransu daga farmakin duk wani abu da zai cutar da su.

Kyankyaso na da saurin da zai iya gudun mita 1.5 cikin dakika daya.

Duk da da dai suna da fuka-fukai, amma ba kowane kyankyaso ne ke iya amfani da fuffukensa wajen tashi ba.

Galibi, kyankyasai sun gwammance gudu a kasa maimakon tashi, saboda ba sa iya yin nisa da tashin nasu, inji masana.

Bincike ya nuna kyankyasai kwari ne masu sha’awar giya, don haka abu ne mai yiwuwa su mamaye kofi ko kwalbar giyar da aka bari a bude muddin suka gano hakan.

Ko cikin firiji aka ajiye giyar har can suna iya shiga su dandana muddin aka bar firijin a bude.

Masana kimiyyar kwari sun ce, kyankyasai na iya rike numfashi na wasu ‘yan mintoci, kana suna iya nutso a cikin ruwa na tsawon minti 30.

Kyankyasai kwari ne da suka fi sha’awar yin kiwo a wajen tarkace da dago-dagon kayan abincin mutane. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa mawuyacin abu ne a rasa kyankyasai a gidaje.

Suna daga cikin kwarin da ke yada cututtuka a cikin al’umma, don haka masana da hukumomin kiwon lafiya kan karfafa wa mutane daukar matakan hana zaman kyankyasai a gidaje don kauce wa cutarwarsu.

%d bloggers like this: