✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastoma ta sace yara 2 a shagon mahaifiyarsu a Binuwai

Ta fake da neman canji ta yi layar zana da yaran su biyu

Wata mata ta ba san ko wace ce ba ta sace wasu kananan yara biyu ’yan shekaru biyu da kuma hudu a shagon mahafiyarsu a garin Makurdi, hedikwatar Jihar Binuwai.

Aminiya ta gano cewa matar ta sace yaran daga shagon mahaifiyarsu ne bayan ta yaudare su ta hanyar yin sayayyar kayan makulashe.

Majiyarmu ta ce matar ta fake ne da sunan sayen kantu a shagon, amma ta ce ba ta da canji, don haka ta bukaci su biyo su karbo kudin, inda daga nan ta yi layar zana da su.

Wani makusancin iyayen yaran mai suna Tica Saviour, ya shaida wa wakiliyarmu a Makurdi cewa, “A shagon mahaifiyar yaran aka sace su bayan ta tafi cocin da ke kusa da su domin ibadar ranar Lahadi ta bar su su kula da shagon, inda take sayar da hatsi da kunu da sauran kayan makulashe.

“A nan ne wata mata ta zo ta sayi kantun N50 ta ba su N500. To kasancewar babu canji sai ta bukaci yaran su biyo ta bakin hanya ta samu canjin ta ba su.

“Daga nan ba a kara jin duriyarta ba ballantana na yaran, amma an kai rahoton lamarin ga Babban Ofishin ’Yan Sanda na Zone B, inda muke fatan jin kyakkyawan labarin dawowar yarana,” in ji Tica Saviour.

Kakakin ’yan sandan Jihar Binuwai SP Catherine Anene, ta tabbatar wa wakiliyarmu ta rubutaceen sako cewa rundunar ta samu rahoton sace yaran, kuma “muna gudanar da bincike a kai.