✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garin da mutum 10,000 ke ganin likita a ƙarƙashin bishiya a Kano

Sama da shekara 10 ke nan da bishiyar ta zama cibiyar kula da lafiya a garin Baita mai yawan al'umma dubu takwas a Jihar Kano.

Sama da mutum 10,000 ke zuwa domin likita ya duba lafiyarsu a ƙarƙashin wata bishiya a ƙauyen Baita da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

Duk da cewa fuskarta na cike da damuwa, Aliya Alƙasim, wata matar aure wadda ta kawo jaririyarta mai fama da rashin lafiya ƙarƙashin wannan bishiya domin karɓar allura, tana cike da fatan samun waraka ga ’jaririyar tata.

Ta shaida wa Aminiya cewa, “Muna fama da ƙalubalen rashin asibiti wallahi. Saboda idan yara ba su da lafiya sai ka rasa inda za ka kai su. Ko cuta ce ta samu mutum, sai yaro ya jigata ko iyayensa sun jigata kafin a samu kai yaro asibiti.”

Sama da shekara 10 ke nan da wannan bishiya ta zama cibiyar kula da lafiya a matakin farko a garin Baita mai yawan al’umma dubu takwas a Jihar Kano. A gefen bishiyar kuma tabarmi ne waɗanda mutane ke zama domin bin layin ganin likita. Haka lamarin yake a kowane yanayi, na zafin rana, sanyi ko damina da sauransu.

A kusa da bishiyar kuma wani shago ne mai ciki biyu, wanda a cikinsa mutanen Baita da mazauna wasu kauyuka 10 da ke maƙwabtaka da su suke zuwa garin domin ganin likita ko awon juna biyu da sauransu.

Mutanen yankin Baita mai yawan al’umma 8,000 sun karɓi aron shagon ne daga hannun wata mata domin ya kasance cibiyar kula da lafiyarsu, bayan lalacewar asibitin sha-ka-tafi da gwmanati ta gina musu shekara 30 da suka gabata.

Bayan shekara 20 da gina asibitin ya daina aiki, yanzu shekara 10 ke nan, alhali a wancan lokacin da shi mutanen yankin suka dogara domin duba lafiyarsu, kafin ya shiga wannan hali. Yanzu an wayi gari asibitin ya koma ɗaki mai ciki biyu da ƙarƙashin wannan bishiya.

Dagacin ƙauyen, Malam Alkasim Isiyaku, ya shaida wa Aminiya cewa “Muna da mutane sun kai dubu takwas, amma waɗanda suka dogara da wannan asibiti za su kai mutum dubu goma. Gaba ɗaya da asibitin muka dogara, nan muke zuwa. Idan ma babu magani za a rubuta maka, je ka wuri kaza ka saya.”

Ya bayyana cewa shagon shi ne na biyu da suka karɓi aro domin kula da lafiyar al’ummarsu, bayan mai shagon farko ya buƙaci amfani da kayansa.

Mai unguwar ƙauyen, Malam Baita Abdullahi, ya bayyana cewa, yanzu kimanin shekara 10 ke nan da al’ummarsu suka tsinci kansu a wannan yanayi, bayan daina aikin asibitin gwmanatin.

Ya ce ginin asibitin gwamnatin yana daf da rushewa sakamakon tsattsagewan da ya yi. Saboda haka, yanzu a ƙarƙashin bishiyar da kuma shagon mutane kimanin dubu 10 daga ƙauyen da maƙwabtansu suke zuwa kula da lafiyarsu tsawon shekara 10.

Jami’an kiwon lafiya bakwai kacal, ciki har da masu aikin sa kai ne suke duba su tare da maƙwabtansu aƙalla mutum 2,000. Ana iya kiyasta cewa kowane jami’in lafiya ɗaya yana matsayin mutum dubu ɗaya da ɗari huɗu.

Mai unguwar Baita ya bayyana cewa, “mun daɗe muna fama da wannan matsala, sakamkon barazanar rugujewar shi wannan asibiti [da gwamnati ta gina].

“Likitocin da ke aiki a wannan asibiti suka ga bai kamata a zauna a cikinsa ba, sai suka zo suka gaya wa Mai Girma Dagaci cewa ga matsalar da ke faruwa. Sai muka kai ƙoƙon bararmu ga wani bawan Allah wanda ke da shaguna ya taimaka. Shi ne ya fara saukar su, suka mayar da kayansu can.

“To ka san harkar rayuwa, mutum ya gina shagonsa ne domin ya amfana, to sai ya buƙaci waɗannan jami’an lafiya su ba shi wannan wurin zai yi amfani da shi. Don haka sai muka rasa inda za mu kai likitocin.

“Sai ita wannan hajiyar ta ga dacewar abin a tattare da al’umma, sai ta sanar wa dagaci, ya je ya ga wurin da za ta bayar, aka umarci likitocin su mayar da kayansu wannan wuri, shi ne suka mayar da gadonsu na kwantar da mara lafiya da kayayyakin kula da marasa lafiya cikin wannan asibiti.”

Ɗaya daga cikin jami’an lafiyan cibiyar, Nazifi Abdullahi, ya ce, idan masu awo suka zo, tunda ciki da falo ne, “muna fitowa waje su kuma su yi harkarsu a ciki. Idan aka samu mara lafiya da ke buƙatar sirri, sai mu shiga daga ciki, su ɗan ba mu wuri mu tautauna da shi.

“Sannan kamar allurar yara da ake yi ta yau da kullum, to nan gindin bishiya muke yi. Idan muka samu mutane da yawa kuma, ga tabarmi nan kamar yadda kake gani, a nan suke jira, idan mutum layi ya zo kansa, zai shiga can ciki a tattauna da shi ya faɗi matsalarsa.”

Ba mu da masaniya —Kwamishinan lafiya

A wata hira da aka yi da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan lamarin saboda ba a sanar da shi halin da asibitin na Baita ke ciki ba a hukumance.

Kwamishinan ya ce, “Ban samu wani saƙo a hukumance daga wurinsu ba, amma yanzu tun da na san halin da ake ciki zan tura mutane su je su ga yadda lamarin ya ke.”

Kwamishinan ya ce jihar na da cibiyoyin lafiya asma da guda 2,000, waɗanda daga cikinsu aka zaɓi guda 11 da za a gyara.

“Zan duba in ga ko suna cikin ayyukan da muka shirya ƙaddamarwa, idan kuma ba su ciki zan yi ƙoƙarin sanya su cikin waɗanda za mu yi nan gaba a watannin farko na shekara mai zuwa.’’

Mun sanar da ma’aikatar lafiya — Ciyaman

Aminiya ta tuntuɓi Shugababan ƙaramar Hukumar Gezawa, Alhaji Muƙaddas Jogana, game da halin da asibitin ƙauyen Baita ke ciki, inda ya bayyana cewa ya ziyarci wuin domin ganin yadda za a shawo kan matsalar kuma ya aika wa Ma’aikata Lafiya ta jihar a hukumance domin ɗaga darajar cibiyar lafiyar.

Ya ce, “Mun yanke shawarar gina cibiyar lafiya mai gadaje goma a wurin. Mun rubuta wa ma’aikatar lafiya a hukumance cewa ga abin da muke so.”