✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta mika motacin yakin da aka kama a iyakar Kamaru ga Amurka

Shugaban Hukumar Kwastam a Jihar Adamawa, Kamarudeen Olumo ya mika motocin yaki masu sulke da aka kama kwanaki bayan shigo da su ta Jihar Adamawa…

Shugaban Hukumar Kwastam a Jihar Adamawa, Kamarudeen Olumo ya mika motocin yaki masu sulke da aka kama kwanaki bayan shigo da su ta Jihar Adamawa zuwa ga mai lura da ayyuka na Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya, Kathleen Fitz Gibbon.

Aminiya ta ruwaito yadda aka  kama motocin a kwanakin baya, ba tare da sanin aihinin masu motocin ba.

Shugaban Kwastam din ya ce Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA) ne ya umarce shi ya mika motocin ga Gwamnatin Amurka.

“Umarni ne daga Mai Bada Shawara kan Tsaron Kasa in mika motocin ga Gwamnatin Amurka,” inji shi.

Da take jawabi, Kathleen Fitz Gibbon ta mika godiyarta ga Gwamnatin Najeriya kan ba su hadin kai wajen mayar musu da motocin.

Ta ce an kama motocin ne a hanyarsu ta zuwa Jamhuriyar Nijar domin ayyukan tsaro.

“Najeriya da Amurka na da kyakkyawar alaka da fahimta a tsakaninsu, motocin na kan hanya ce  zuwa Nijar domin gudanar da ayyukan tsaron,” inji ta.

Ta yi godiya kan yadda gwamnatin Najeriya ta adana motocin sannan ta ce jirgin Amurka na sojoji zai zo ya dauki motocin zuwa Nijar.

A lokacin da ake mika motocin yakin akwai manyan jami’an tsaro da dama da suka hada da Manjo Peter Shayborn na kasar Amurka.

A watan Agusta ne aka kama tankokin yaki shida a garin Konkol da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, a Hukumar Maiha a Jihar Adamawa.