✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwastam ta kwace kayan N40m a Kaduna

An kama tabar wiwi kulli 433 da shinkafar waje buhu 373 da sauran haramtattun kaya.

Hukumar Kwastam ta Kasa (NCS) ta kwace kayan da aka yi fasakwaurinsu da kudinsu ya kai Naira miliyan 40.530 a Kaduna.

Kwamturolan Shiyya ta biyu ta Hukumar, Al-Bashir Hamisu, ya ce haramtattn kayan da suka kama sun hada da tabar wiwi kulli 434, shinkafar waje buhu 373, jarkokin mai gyada 45, da dila 48 na tufafin gwajo.

“Darajar kayan ta kai N40,526,273. Sakona ga masu fasakwauri shi ne ba za mu kyale su ba, za mu bi su har makwancinsu don mu hana shigo da shinkafa da sauran haramtattun kaya cikin wanan kasa,” inji shi.

Al-Bashir ya ce hukumarsa ta mika tabar wiwin da ta kama ga Kwamandan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), reshen Jihar Kaduna, Uche Iyke.

Kwamnandan na NDLEA ya jinjina wa Hukumar Kwastam din, inda ya kara kira gare ta da ta kara jajircewa domin dorawa a kan gagarumar nasarar da ta samu.

Da yake bayani a Ofishin Shiyyar da ke Kaduna, Al-Bashir ya ce, Hukumar za ta ci gaba da jajircewa a kan ayyukanta a kan iyakokin Najeriya domin dakile ayyukan masu fasakwaurin kaya zuwa kasar.