Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kwace bindigogi da albarusai bayan musayar wua da masu fasakwaurinsu kaya zuwa Najeriya.
Kwanturolan Kwastam na Shiyyar A, Hussein Ejibunu, ya ce jami’an da ke aiki a Sashen Bincike (FOU) sun kwace makaman ne bayan dauki-ba-dadi a yankin Idi-Roko, Jihar Ogun.
- An cafke dan Najeriya da ya aikata fashi sau 68 a Amurka
- Gwamnoni da Kwamitin Amintattun APC sun sa labule
Ya shiyyar ta yi nasarar kwato Naira miliyan 107.8 na harajin da aka ki biya na wasu kayayyakin da aka tantance a tashoshin jirgin ruwa da kuma iyakokin kasa na kan tudu.
Hussein Ejibunu, ya ce a watan da ya gabata sun kama kaya da yawa da aka shigo da su kasa ba a bisa ka’ida ba, wanda a kiyasce harajinsu ya kai miliyan N633.4.
Kayayyakin sun hada da shinkafar waje buhu 7,328, man fetur lita 121,550, katan 68 na naman kaji da kuma katan 37 na kwai.
Sauran su ne, tabar wiwi mai nauyin kilogram 150, jakunkunan sojoji 10, dila 1,955 na gwanjo sai kuma kananan motoci guda shida, duka a cikin watan Satumban da ya gabata.