✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwastam ta kama tabar wiwi ta biliyan N1 a Legas

Tabar wiwin mai nauyin ton shida shi ne na biyu mafi muni da aka kama a Legas.

Jami’an Hukumar Kwastam at Najeriya sun kama tabar wiwi da kudinta ya kai Naira biliyan daya a ranar Juma’a.

Kame tabar wiwi mafi muni na biyu ke nan da Hukumar aka yi a gabar teku a Legas, inda a wannan karon aka kwace tabar wiwin da nauyinta ya kai ton shida.

Sashen Tsaron Lafiyar Ruwa na Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke Legas, ya sanar da haka ne ta bakin Kwamandan yankin, Peters Olugboyega, yayin da yake jawabi ga manema labarai a Legas.

Karin bayani zai biyo baya.

%d bloggers like this: