✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama shanu da kayan Naira miliyan 76 a Kano

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam, da ke kula da shiyyar Kano da Jigawa ta bayyana sabbin matakan da ta dauka na masu amfani…

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, Kwastam, da ke kula da shiyyar Kano da Jigawa ta bayyana sabbin matakan da ta dauka na masu amfani da shunu don yin safara tare da shigo wa da shinkafar waje zuwa kasar.

Kwantirolan shiyyar na Hukumar Kwastam Nasir Ahmed ne ya sanar da hakan lokacin da ake bayyana irin shanun da kama, sannan ya sanar da cewa, an kama kayan da aka shigo da su ta gurbatacciyar hanya da ya kai Naira miliyan 76.