✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa

Akalla mutum biyar ne aka bindige a fada tsakanin jami’an kwastam da ’yan sumoga a ranar Sallah Karama.

Akalla mutum biyar ne aka bindige a sabon fadan da aka gwabza tsakanin jami’an kwastam da ’yan sumoga a ranar Sallah Karama.

Shaidu sun ce jami’an kwastam sun bude wuta ne ranar Alhamis da yamma bayan wata motar fasakwaurin shinkafar waje ta nemi tsere musu zuwa babban garin Iseyin.

Wani mazaunin Iseyin, Kehinde Adekunle, ya ce: “Gaskiya ne. Jami’an kwastam din sun bude wuta a lokacin da suke kokarin kama wata motar kayan fasakwauri da ke shigowa daga kan iyaka.

“A kan idona abin ya faru. Akwai wasu dattawa biyu da ke shagulgulan sallah da wasu karanan yara ne abin ya ritsa da su.

“Duk da cewa ba su din aka harba kai tsaye ba, amma bai dace su kwastam din su yi harbi a wurin da ke cike da mutane haka ba, ga shi kuma ranar Sallah ce, duk mutane sun fito suna bukukuwa.

“Abin da ya tayar da hankulan mazauna yankin da iyalai da abokan arzikin mutanen har suka fara zanga-zanga.”

Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne a yankin Oja-Oba, inda ’yan sumogan na isowa da motar shikafar, sai jami’an na kwastam suka bude wuta, suka kashe wasu mutum hudu da ke gudanar da shagulgulan sallah.

Shi ma wani dan garin Iseyin, Alhazan Kamorudeen da ke hanyarsa ta komawa gida daga Ibadan a lokacin da muka tuntube shi, ya ce: “Gaskiya ne. Na kira mutane a gida sun kuma tabbatar min da faruwar lamarin, kuma hankula sun tashi.”

Wasu matasa ’yan asalin yankin Oke-Ogun na daga cikin wadanda suka gamu da ajalin a yayin da jami’an na kwastam suke artabu masu fasakwaurin a yankin na Iseyin a Karamar Hukumar Iseyin ta Jihar Oyo.

Sarkin kasar Iseyin, Abdulganiyy Adekunle Salau, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kira ga jami’an kwastam su ba da tazarar kilomita 40 daga iyakan garin.

Aseyin ya bayyana takaicinsa kan abun da ya faru a ranar Sallar, yana mai kira da ga gudanar da cikakken bincike domin kauce wa aukuwar irinsa a nan gaba.

Mai magana da yawun hukumar kwastam reshen Oyo, Kayode Way bai samu amsa sako ko kiran wayan da muka yi masa ba domin tabbatar da hakikanin abin da ya faru. Haka shi ma takwaransa na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Adewale Osifeso.