✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam sun kama katon 38 na kwayar Tiramol a Jigawa

Jami’an hukumar Kwastam a Jihar Jigawa sun kai samame bakin bodar Maigatari, inda suka sami nasarar kama kwayoyin Tiramol katan 38, da aka yi kiyasin…

Jami’an hukumar Kwastam a Jihar Jigawa sun kai samame bakin bodar Maigatari, inda suka sami nasarar kama kwayoyin Tiramol katan 38, da aka yi kiyasin kudinsu sun kai Naira miliyan N20m. An boye akwatunan kwayoyin ne a cikin karmamin kara, a wata gona da ake zaton ’yan fasa kwauri ne suka boye.

Babban jami’in Kwastam mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Alhaji Yusuf Abba Kassim ya sanar da manema labarai haka, a lokacin da ya kira taron manema labarai a babban ofishinsu da ke Kano. 

Ya ce sun sami labarin shigowa da miyagun kwayoyin ne ta hanyar wasu masu kishin kasa da suka bayyana haka ga hukumar. Ya kara da cewa wadanda suke aikin fasa kwaurin suna amfani ne da amalanken shanu suna saka katon-katon na kwayoyin kuma su lodo kara a bisa, har suka tara katon 38 a wata maboya, suka lullube da kara.

Ya kara da cewa sun sami nasarar kama kwayoyin ne a wata gona da ke kan hanyar kauyan Galadi zuwa garin Birniwa suka bude karan suka kwashe kwayoyin amma ba su sami wanda ya mallake su ba. Sai dai ya yi alwashin cewa suna nan sun baza koma domin nasarar kama shi.