✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwankwaso ya jagoranci taron kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa

Kwankwaso ya ce sun shirya don tunkarar zaben 2023.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kaddamar da wani gangami da ake wa take da ‘The National Movement’ (TNM), don yin sabuwar tafiya a siyance.

Sabuwar kungiyar siyasar ta samu tagomashin manyan ‘yan siyasa daga sassan kasar nan da suka hada da Kyaftin Idris Wada, Lucky Ignedion, Adamu Aleiro, Saminu Turaki, Donald Duke, Liyal Imoke, Abdulfatah Ahmed, Serika Dickson, Attahiru Jega, Solomon Dalung, Buba Galadima, Sanata Rufai Hanga da sauransu.

Taron ya wakana ne a dakin taro na International Conference Centre da ke birnin tarayya na Abuja a ranar Talata.

Da ya ke jawabi yayin taron, Kwankwaso, ya ce sun hada kai ne da sauran masu kishin Najeriya don ceto ta daga halin da ta fada.

A cewar Kwankwaso za su dukufa wajen farfado da tattalin arzikin kasar nan da inganta rayuwar ‘yan kasa a birni da karkara

Kazalika, ya jadadda cewar sun shirya tsaf domin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Har wa yau, Kwankwaso, ya ce za su yi wa makiyaya gata na ganin cewa ba a cin ye musu burtalai ba, sannan za su bai wa manoma dukkan kariyar da su ke bukata.

Manyan ‘yan siyasa da suka halarci taron sun nuna jin dadinsu, da yin jawabai na tunkarar babban zabe a 2023.

Ana ta rade-radin tsohon gwamnan na Jihar Kano, zai fice daga jam’iyyar PDP sakamakon takun saka da ya ke samu da wasu ‘ya’yan jam’iyyar.

Sai dai Kwankwaso bai bayyana shirin ficewa daga jam’iyyar ba.

Amma a makon da ya gabata ya bayyana cewar jam’iyyar APC da PDP babu wani abu da suka amfana wa ‘yan Najeriya da za su sake zabensu a 2023.