✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwasiyya ta kai karar Ganduje kan bashin Biliyan N399

Kungiyar siyasar nan ta Kwankwasiyya karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta yi barazanar maka gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ta yi barazanar maka Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da gwamnatinsa a gaban kuliya idan har ta ci gaba da kokarin karbo bashin Yuro miliyan 684, kwatankwacin Naira biliyan 339.

Tun da farko Gwamantin Ganduje ta rubuta wa Majalisar Dokokin Jihar neman sahalewar karbo rancen daga Bankin Kasar China don gudanar da aikin hanyar dogo.

Kwankwasiya a sanarwar akakinta kuma dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar PDP a zaben 2019 Kwamaret Aminu Abdussalam, ya fitar ta nuna takaicinta kan mataki da ta bayyana da cewa abin kunya ne.

A cewarta, bashin wanda za a biya shi cikin shekaru 50 ko sama da haka zai iya jefa rayuwar al’ummar Kano cikin kangin bashi da wahalar da ba a san iyakarta ba.

“Duk da matsin rayuwa da ake fuskanta da rigimar canjin kudaden kasashen waje da talauci da ake fuskanta da masassarar tattalin arziki da cutar coronavirus ta haddasa, amma gwamnati ta gwammace ta yi amfani da kudaden harkar ilimi da lafiya da sauran kayayyakin more rayuwa na al’ummar da za ta zo nan gaba ta hanyar kakaba musu bashi”, inji sanarwar.

Ya ce kungiyar da jami’iyyar PDP a jihar ba za su lamunci karbo bashin ba domin a cewarsu karkatar da kudden za a yi.

Da take kira ga masu ruwa da tsaki su hada kai su hana karbo bashin, Kwankwasiyyar ta ce tuni ta dauki matakin sanar da Bankin Kasar China game da haramcin da ke cikin karbar bashin.

“Mun rubuta wa ofishin Jakadancin China a Najeriya game da hadarin kulla waccan yarjejeniya da Ganduje.

“Mun rubuta wa Shugaban Majalisar Dattijai da Ministan Kudi da Shugaban Hukumar kula da Basussuka ta Kasa game da bautar da al’ummar Jihar Kano da ake shirin yi ta hanyar karbo wancan bashi.

“Har ila yau lauyoyinmu sun shigar da kara gaban kotu don kalubalantar halalcinsa da kuma karya dokar karbar bashin da ake shirin yi”, inji Kwankwasiyya.