Bayanai na nuni da cewa nan ba da jimawa ba za a fara tattaunawa tsakanin Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar.
Majiyoyi sun ce za a sanar da sabuwar ranar da za a yi tattaunawar ce da zarar malaman addinin Musuluncin da suka tattauna da gwamnatin sojin a birnin Yamai suka gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ke Hana Matasan Najeriya Cigaba
- Ruwan sama ya karya gadar da ta hada Bauchi da Gombe
Ana sa ran tawagar malaman, wacce ke karkashin jagorancin shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, za ta gana da Tinubu a [yau] Litinin domin yi masa bayanin abin da ya wakana.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce ECOWAS ta yi maraba da tattaunawar da kuma yadda sojojin suka rungumi sulhu hannu bibbiyu.
Rahotanni sun ce yayin tattaunawa da malaman, shugaban gwamnatin sojin, Janar Abdulrahmane Tchiani, ya nuna a shirye suke su hau teburin sulhu da ECOWAS.
Bugu da kari, wata majiya a Fadar Shugaban Najeriya ta shaida wa Aminiya cewa, “Tinubu na matukar son ganin an lalubo bakin zaren rikicin siyasar Nijar.
“A takardar bayan taron da ECOWAS ta fitar a ranar Alhamis, ta nuna cewa tana fatan ta ga an samo maslahar wannan rikicin cikin ruwan sanyi, saboda haka wannan ba wai kawai maganar Fadar Shugaban Kasa ba ce. Muna maraba da hawa teburin sulhu.
“Tattaunawar na daya daga cikin matsayar da aka dauka a yayin wancan taron na karshe. Duk da cewar sun ba da dakarunsu umarnin kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana, amma sun bude kofar tattaunawa,” in ji majiyar.
Daga Isiaka Wakili, Seun Adeuyi, Dalhatu Liman (Abuja) da Sani Ibrahim Paki