Gwamnatin Tarayya ta ce ta shirya tsaf domin dawo da zirga-zirgar kasa da kasa a filayen jiragen sama na biranen Kano da Fatakwal.
Hakan na zuwa ne bayan shafe akalla watanni uku da bude filayen Legas da Babban Birnin Tarayya Abuja.
- Makiyayi zai yi wata 6 a daure saboda shanunsa sun shiga filin jirgi
- Jirgin soji ya yi hatsari a kasar Masar
Babban daraktan Hukumar Dake Kula Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA), Kaftin Musa Nuhu ne ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabin Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa domin yaki da cutar COVID-19 ranar Alhamis.
A cewarsa, za a bude filayen ne da zaran an shawo kan matsalolin da ke addabarsu na karancin isassun kayan aiki da ma’aikata.
Ya ce za a sake bude filayen ne da nufin ganin an rage cinkoson da ake fama da shi a na Legas da Abuja.
Sai dai bai bayyana takamaiman ranar sake bude su ba.
Shi kuwa da yake jawabi, shugaban Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu shawartar ‘yan Najeriya ya yi kan su rage tafiye-tafiyen ba gaira ba dalili nan da shekara daya mai zuwa.
Ya ce kiran ya zama wajibi la’akari da yadda mutane su ka saba yawan tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare, musamman lokacin bukukuwan Kirsimeti.