✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana biyu bayan dawowarsa daga Saudiyya, Buhari ya wuce kasashen Turai

Shugaban zai halarci taro kan sauyin yanayi a Scotland, sannan ya wuce Faransa

Kwana biyu bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya inda ya halarci wani taron zuba jari tare da yin Umarah, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya wuce birnin Glasgow na Scotland.

Shugaban dai zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya ne karo na 26 ne kan sauyin yanayi, wato COP26, kafin daga can kuma ya wuce birnin Paris na Faransa.

Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi, ya ce Buhari zai gabatar da jawabi ga Shugabannin Kasashe a taron ranar Talata.

Shehu ya ce taron dai zai tattauna matsayin Najeriya kan yunkurin magance kalubalen sauyin yanayi, ya kuma yi bayani kan ci gaban da kasar ke samu wajen rage amfani da makamashi mai fitar da hayaki.

Taron, wanda Birtaniya za ta karbi bakuncinsa da gudunmawar Italiya, zai tattaro kasashe wuri guda da nufin tattauna ci gaban da ake samu wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris.

Kakakin ya kuma ce bayan kammala taron na Scotland, Buhari zai wuce birnin Paris a wata ziyarar da ramuwa ga wacce Shugaban Kasar, Emmanuel Macron ya kawo Najeriya, sannan kuma ya halarci Taron Zaman Lafiya na Paris, wanda Macron din zai shirya.

Yayin ziyarar dai, Shugaba Buhari zai sami rakiyar Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Minista a Ma’aikatar Muhalli, Sharon Ikeazor; mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da kuma Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.