✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwana 30 a hannun ’yan bindiga: ‘Yaro ya rika kuka a bar shi ya kashe mu’

'Muna zargin direban da ya dauko mu yana yi wa ’yan bindiga aiki'

Malam Hassan M. Sagir da aka fi sani da Musan Alin Shehu, malamin makarantar firamare ne da ya kwashe kwana 30 a hannun masu garkuwa da mutane a dajin Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

A tattaunawar da Aminiya ya bayyana irin azabar da suka sha a dajin da yadda suka tsira:

– Yadda aka sace mu

Da farko sunana Hassan M. Sagir, amma wadansu sun fi sani na da Musa Alin S-hehu.

Ni mutumin garin Kafanchan ne a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Ina koyarwa a makarantar firamare a Jama’a kafin a yi wa malaman firamare jarrabawa na samu maki 74, amma aka kore ni tare da wasu cewa mun fadi a jarrabawar.

Daga baya aka bayar da dama ga wanda zai sake jarrabawar na sake na ci daga nan aka sake dauka ta aikin koyarwa aka mayar da ni Karamar Hukumar Birnin Gwari bayan an rage min matsayi daga mataki na 13 zuwa na 7.

Tun daga shekarar 2018 na ci gaba da zuwa koyarwa a Birnin Gwari.

To kowa ya san hanyar Birnin Gwari ta dade da zama sansanin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ta yadda duk wanda ya kama hanyar zuwa Birnin Gwari akan ce ya kama hanyar shahada.

Bayan an biya mu albashin watan Yuli mun je sai aka ce sai mun koma Birnin Gwari don a tantance mu.

To mun kama hanya ranar Litinin 2 ga Agustan da ya gabata, mun shiga motar Birnin Gwari a tashar da ake kiran ta Mando a Kaduna, muna cikin tafiya a dajin Birnin Gwari sai muka yi gamo da ’yan bindiga hudu suka tsare titi dauke da manyan bindigogi.

Nan direban ya taka birki ya bude kofa ya fita a guje sai suka yiwo kanmu suka fitar da mu suka kwantar a kan titi.

Tun daga nan ne sai muka fara zargin anya direban da ya dauko mu ba yana yi wa ’yan bindigar aiki ne ba kuwa?

Mun yi zargin haka ne ganin yadda yana kawo mu ya fita a guje kuma babu wanda ya damu da shi a cikinsu, sai muka tuna ai tunda ya dauko mu yake ta faman yin waya a hanya babu kakkautawa.

Daga nan suka tasa keyarmu zuwa cikin daji. Mun kwashe kusan awa biyar ana tafiya da mu, mu shida; maza uku, mata uku.

Tun misalin farfe 10:30 na safe ake tafiya da mu ana dukan mu har zuwa farfe 5:30 na yamma.

Sai suka ajiye mu a wurin suka ce duk wanda bai yi gardama ba, ba za su taba shi ba.

– Sun azabtar da mu sosai a dajin

Bayan sun zaunar da mu a fili, sai suka daure kafafu da hannuwanmu kuma suka rufe mana fuskoki.

Sun yi ta dukan mu da sanduna a tafukan kafafunmu suna tambayarmu aikin da muke yi da abin da muka mallaka.

Na ce musu ni da wanda muka taho malaman firamare ne.

Da farko sun ki yarda suna cewa, ni mai kudi ne sai na fada musu gaskiya.

Sun ja abokin tafiya ta wani wuri suna azabtar da shi cewa, sai ya fada musu cewa ni mai kudi ne.

A haka dai daga baya suka yarda cewa mu malaman makaranta ne bayan sun kira wani da ya yi karatu a cikinsu ya duba takardunmu.

Suka ce tunda muna koyarwa a makarantar gwamnati ai gwamnanmu ya san damu don haka dole za su samu kudi a kanmu a wajen gwamnati.

Suka karbi wayata suka duba hotuna da kayan da nake sanyawa suka ce atafau ba su yarda ba, ni mai kudi ne.

Kullum suna azabtar da mu da duka a tsakiyar daji babu rumfa haka muke kwana mu wuni da sanyi da rana da iska da raba da ruwan sama duk a kanmu suke karewa, baya ga sauro da sauran kwari da suke cizon mu.

Ba kukan dabbobin gida, ballantana ka yi tunanin kana kusa da gari ko kauye.

Mukan dai ji kukan dabboin dawa irinsu kura da tsuntsaye, kuma muna ganin sawayen wasu dabbobi idan za mu je dibo itace don jin dumi.

– Sau daya suke ba mu abinci a wuni

A kullum sau daya kawai suke ba mu abinci wanda mu suke sawa mu dafa da kanmu. Ko shinkafa ko taliya abincin ba ya wuce cikin tafin hannu. Wani lokaci a sa manja da magi wani lokaci haka mu ke ci. A wani lokaci ma ko gishiri ba a sanyawa.

Kuma duk tsawon lokacin da muka shafe a dajin ba su taba barin mu mun yi Sallah ba.

Sukan ce ba a yin ibada a wurinsu kuma duk wanda ya kuskura suka kama shi yana ibada, to ya kuka da kansa.

Haka muka zauna kwana 30 ba wanka ba wanki ba alwala ba Sallah.

Amma kuma a rediyo MP3 dinsu za ka ji suna sa wa’azozin malamai daban-daban da tafsirai da kasidu amma ba sa ibada.

– Mun yi yunkurin gudu ba nasara

Akwai lokacin da muka yi yunkurin gudu daga dajin sai dai ba mu yi nasara ba, kuma a dokarsu duk wanda ya yi yunkurin gudu aka kama shi, hukuncinsa kisa ne.

Wani dare mun kaikaici yaran da aka sanya su yi gadinmu, kanana ne kuma saboda an fara sabawa da mu sai ba su rike bindiga ba sai adduna.

Da muka ga sun yi barci misalin karfe 4:00 na asuba sai mu ukun maza muka sulale muna ta gudu a cikin daji ba mu isa bakin hanya ba sai misalin karfe 8:30 na safe.

Ba mu sani ba ashe sun hau babur sun shawo kanmu kawai sai muka gan su sun ritsa mu, haka suka sake mayar da mu.

Allah Ya taimake mu kansu ya rabu; wadansu suka ce a kashe mu wadansu kuma suka ce a kyale mu.

Akwai yaron da yake ta kuka don me za a hana shi ya kashe mu.

Nan suka sake shigar da mu can cikin daji suka daure mu.

Bayan an tambayi wanda ya shirya guduwar duka biyun suka ce, babu ruwana, na ce kada a gudu amma da na ga za su gudu shi ne ni ma na bi su.

A nan dai aka yi musu muguwar azabar da sai da suka kwashe mako guda ba sa moruwa. Kusan komai ni nake yi musu.

Kuma idan mutum ba ya da lafiya a dajin nan babu wani tanadi na magani.

– Dalilin da suke ta’addanci

A wani lokaci muna hira da wadansu masu dan sassaucin ra’ayi a cikinsu, sai suka fada mana cewa, su abin da ya sa suke aikata wannan aika-aikar shi ne, su ma an taba yin garkuwa da iyayensu kuma an sace musu dabbobinsu, ko an kashe musu iyaye tare da raba su da duk abin da suka mallaka.

Suka ce abin da ya sa suka shiga harkar garkuwa da mutane ke nan.

Akwai wani ma a cikinsu da ya ce mana shi ba a son ransa yake wannan aiki ba.

Akwai wanda ya ce min, “Malam shin wannan aikin da muke yi idan mun mutu za mu samu rahamar Ubangiji kuwa?”

Na ce musu ko za su kashe ni sai na fada musu gaskiya duk wanda ya mutu a wannan hanyar wuta zai shiga kai-tsaye.

Shi ne suke ce min to in taya su da addu’a su bar wannan aikin kuma mu daina yi musu mummunar addu’a ko da mun dawo gida.

– Yadda suke raba kudin fansa

Yadda suke yi idan sun karbi kudi shi ne su wadanda suka fita aiki da bindiga da wadanda suka bayar da bindiga aka yi ta’asa aka samu kudi to suna rabawa daidai ne da su.

Wato idan ka bayar da bindigogi mutum biyar suka kamo wadansu kuma aka samu kudi, to abin da aka raba wa mutane biyar din haka za a raba wa bindigogin su ma a kai wa mai shi kamar ya je.

Idan ka ba da bindiga biyu za a ba ka kason mutum biyu haka ko bindiga nawa ka bayar za a ba ka kason kowace.

Hakan ne ya sa kowa a cikinsu yake da burin sayen bindiga wadda suka ce kudin kowace yana kamawa ne daga Naira miliyan daya kuma suna sayen harsashi kowane daya a kan Naira 1,500.

– Ba na goyon bayan sulhu da ’yan bindiga

Maganar gaskiya kowa da yadda yake kallon lamarin.

Amma a gaskiya ra’ayina shi ne yadda ba sa sassauta wa mutane idan suka kama komai talaucinka sai sun tatse ka sun azabtar da kai wani ma su kashe shi idan ba su samu abin da suke so ba, to su ma hukuncin da ya dace da su ke nan.

Babu sassauci a tsakaninsu da hukuma.

– Yadda na kubuta daga hannunsu

To su matan sun riga mu fita. Mace ta farko saboda ciwon mele da ke jikinta suna kyamarta ko mako guda ba ta yi ba aka kawo Naira dubu 60 suka sallame ta.

Sauran mata biyun ma kwana 13 aka hado Naira dubu 60 su biyun aka sake su da yake dukkanmu talakawa ne.

Shi daya namijin kuma da ya shirya gudu ya riga mu fita bayan an kawo kudin fansa Naira dubu 200.

Mu biyun kuma, ni da Abdul’aziz I’shaq, sai bayan mun cika kwana 30 bayan an kawo kudin fansa Naira dubu 600 da babura biyu.

Suka goyo mu a baburansu zuwa wani kauye da ake kira Masallaci a gaban Buruku suka hadu da ’yan uwanmu suka karbi baburan suka buga suka tabbatar da lafiyarsu sannan suka fada musu inda za su bi, mu ma suka fada mana inda za mu bi mu hadu da ’yan uwanmu.

Daga nan suka hadu da ’yan uwanmu muka shiga mota da sauri muka dawo gida Kafanchan.

Sun karbe dukkan tufafinmu da wayoyinmu, mutanen kauyen sun yi ta yi mana jaje suna mu yi sauri mu bar wurin don wata tawagar masu garkuwar tana iya sake awon gaba da mu idan suka gan mu.

– Kira ga gwamnati da jami’an tsaro

Kirana gare su shi ne su ji tsoron Allah.

Ba yadda za a yi Bafulatanin da ke zaune a daji ya samu bindiga idan ba da hannun bara-gurbin jami’an tsaro ba.

Dama an ce sai bango ya stage kadangare yake samun wurin shiga

– Ga matafiya

Duk tafiyar da mutum zai yi ya rika yin addu’a sosai.

Sannan idan mutum ya ji wani kishi-kishin a hanya to ya hakura ya canja hanyar duka, tafiya idan ba ta zama dole ba to a hakura da ita.

Sannan a rika lura da irin motocin da za a shiga da wurin da za a shiga mota da irin wayoyinsa za ka ji direban ko yaron mota ko wasu fasinjoji na yi.

– Kira ga ’yan bindiga

Duk da za ka ji suna kawo dalilansu na cin zali da cin zarafin da jami’an tsaro suke yi wa mutanensu a daji idan wata rigima ko wani abu ya hada su da wani ko wadansu, amma duk da haka bai kamata su dauki mataki mai tsauri a kan kowa da kowa ba.

Sannan ina kira ga jami’an tsaro idan wani abu ya faru da wata kabila da Fulani to a daina daukar Fulani a matsayin wadanda ba su waye ba ana cutar su ko ana zaluntar su kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Su kuma masu aikata irin wannan ta’asa na tare hanya suna garkuwa da mutane su ji tsoron Allah.

Kuma gwamnati ta rika lura da jin dadinsu.