Cikin kwana 100 da fara bullar cutar coronavirus a Najeriya, kasar ta ninka yawan cibiyoyinta na gwajin cututtuka masu yaduwa sau goma.
Yanzu Najeriya na da cibiyoyi 30 na gwajin cutar mai sarke nunfashi daga guda uku rak da take da su a sadda cutar ta fara bayyana a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 a kasar.
A ranar Asabar 6 ga watan Yuni ne Najeriya ta cika kwana 100 da fara samun bullar cutar wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana a matsayin annoba a fadin duniya.
Hakika annobar ta kawo sauye-sauye da dama a yadda ake gudanar da kusan dukkanin al’amura, baya ga irin fadi tashin da ake ta yi sakamakon annobar.
Sakaren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya yi karin haske yayin ziyartar Cibiyar Gwajin Cututtuka ta Kasa da ke Gaduwa, a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya jagoranci Kwamitin Ko-ta-Kwana da Shugaban Kasa ya nada domin yakar cutar ta COVID-19 (PTF) ne zuwa Cibiyar da ke karkarshin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) a ranar cikar cutar coronavirus kwana 100 a Najeriya.
Ya ce PTF ta kai ziyararar domin yaba muhimmiyar rawar da cibiyar gwajin ke bayarwa a yaki da COVID-19.
Mustapha wanda shi ne ke Shugaban PTF, ya kuma bayyana wasu matakan da suka biyo bayan bullar COVID-19 a Najeriya, wadda Ministana Lafiya Osagie Ehanire ya sanar a ranar 28 ga watan Fabrairu.
— COVID-19 ta dagula lissafi
Da bullar cutar, Najeriya ta fara tunkarar ta a matsayin annoba a kasa ta fuskoki daban-daban karkashin jagorancin NCDC.
Hukumar ta ayyana annobar a matsayin a mataki na uku —kololuwar matakin yaki da abboba a kasar.
An yi jinyar wanda ya fara harbuwa da cutar a Najeriya ne a cibiyar kula da masu cutar ta farko da ke Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (IDH) da ke Yaba a jihar Legas.
A ranar 28 ga watan Fabrairun ne NCDC ta tura tawaga biyu na ma’aikatan lafiya zuwa jihohin Legas da Ogun domin ganowa, killacewa da kuma jinyar mai cutar na farko da kuma mutanen da suka yi mu’amala da shi a jihohin biyu.
— Fara bullar cutar a Najeriya
Mustapha ya ce COVID-19 ta kawo sauye-sauye a duniya, tare da bankado gaskiya game da bakuwar cutar ta coronavirus da yadda take yaduwa.
A ranar 27 ga Fabrairu, 2020 ne aka gano wani dan kasar Italiya mai shekaru 44 jihar Legas dauke da kwayar cutar. Mutumin shi wanda aka fara ganowa yana da cutar a Najeriya tun bayan bullarta a kasar China a watan Janairu.
“Ya sauka a Filin Jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas daga Milan, Italiya, da karfe 10 na daren ranar 24 ga Fabrairu a jirgin kamfanin Turkish Airline.
“Daga nan ya yi tafiya zuwa kamfaninsa a jihar Ogun a ranar 25 ga watan. Washegari ya fara nuna alamun cutar a wani asibiti a jihar Ogun, inda likitan ya kyautata zaton cutar ce.
“Daga nan aka tura shi IDH a Legas inda aka tabbatar ya kamu da cutar a ranar 27 ga watan”, inji shi.
Gwamnatin Tarayya ta kirkiro PTF domin bayar da dauki kan cutar COVID-91 a Najeriya. A matakin jiha kuma an yi tsare-tsaren bayar da dauki.
— Kara karfin yakar cutar a Najeriya
Ya ce NCDC ta kuma ci gaba da kara yawa da karfin dakunanta na gwaje-gwaje a fadin Najeriya kasancewar kasar ta bayar da muhimmanci ga alkinta damar samun gwaji domin yakar annobar a kasar.
“A baya dakunan gwaji cututtuka masu yaduwa uku ne rake a fadin Najeriya.
“Bayan kwana 100 da bullar cutar yanzu kasar na da dakunan gwaji guda 30”, inji Boss Mustapha.
Sakataren Gwamnatin ya bayyan gamsuwa da yadda NCDC ke yakar cutar, a tsawon lokacin.
Ya kuma jaddada shirin gwamnati na fadada yakinta da cutar ta yadda kowace jiha za ta samu dakin gwajin cutar.
— Yadda NCDC za ta ci gaba da yakar coronavirus
A nasa bangaren Shugaban NCDC Dokta Chikwe Ihekweazu ya ce a kokarin Najeriya na kara karfinta na gwajin cututtuka masu yaduwa, NCDC za rika aiki tare da Cibiyar Nazarin Lafita ta Najeriya (NIMR) da Hukumar Masu Gwaje-gwajen Lafiya ta Najeriya (MLSCN) da sauran kawayenta wurin gudanar da gwaje-gwaje da fitar da sakamako.
Chikwe Ihekweazu ya kara da cewa babban dakin gwaje-gwaje na kasa shi ne ke da alhakin gudanar da gwajin cututtuka da suka addabi al’umma.
— Jinjina ga ma’aikata da hukumomin lafiya
“Tun sadda aka fara samun bullar cutar kwanaki 100 da suka wuce ma’aikatan lafiya ke gaba-gaba a wannan yaki.
Ya kara da cewa, “Muna jinjina wa kwamitocin ko-ta-kwana na jihohi da cibiyoyin ayyukan gaggawa da ayarinsu da masu gwaje-gwaje da daukacin ma’aikatan lafiya da ke aiki ba dare ba rana domin kula da lafiyar jama’a a fadin kasa”.
— Hadin gwiwar yaki da COVID-19
Ya ci gaba da cewa NCDC a shirye take ta yi aiki karkashin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da hadin gwiwar ma’aikatun lafiya na jihohi da sauran ma’ikatu da hukumomin gwamnati ta hanyar PTF, wajen ingantawa da fadada yakin da Najeriya ke yi da wannan annoba.
“Dabarar da muka dauka ita ce tabbatar da ganin karin mutane na samun gwaji da kuma hanzarta zakulo wadanda suka yi hulda da masu cutar da jinyar masu ita domin dakile yaduwarta.
— Mafita a halin rashin magani
“Kasancewar har yanzu babu rigakafin cutar, babu zabin da ya wuci kula da matakan kariya da yanayin mu’amala a cikin jama’a da kuma karfafa masu fama da cutar”.
Don haka ya bukaci kowane dan Najeriya ya bi shawarwarin jami’an lafiya na kauce wa yaduwar cutar da suka hada da tsaftace hannu da sunadaren kashe kwayoyin cuta; rufe fuska da takunkumi a cikin taron jama’a da kuma bayar da tara na akalla mita biyu, da dai sauransu.