✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwana 100 a ofis: Gwamna Matawalle ya ciri tuta

  A yau ne Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawallen Muradun kamar sauran gwamnonin da aka zaba  a bana suke cika kwana 100 a karagar mulki.…

 

A yau ne Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawallen Muradun kamar sauran gwamnonin da aka zaba  a bana suke cika kwana 100 a karagar mulki. Kowane Gwamna da irin rawar da ya taka, amma Hausawa na cewa idan ana dara, fidda uwa ake yi.

Jihar Zamfara ta dade tana fama da matsalolin da suka shafi tsaro, mutanen jihar sun kasance cikin tsoro maimakon tsaro, ga rudani da rashin tabbas musamman na kashe-kashe da sace-sacen mutane,  a daidai lokacin da suke cikin wannan yanayi ne, sai Allah Ya kawo musu jajirtaccen Gwamna, wanda cikin ikon Allah a cikin wadannan kwana 100 ya sa hankalin mutanen jihar ya kwanta.

A kullum ba a samun ribar dimokuradiyya, sai da zaman lafiya. Don haka lokacin da Gwamnan ya yanke shawarar yin sulhu da ’yan bindigar da yawan mutane sun dauka cewa siyasa ce kawai za a yi, domin wadansunsu suna cewa an dade ana ruwa kasa na shanyewa. Amma kuma sai Allah Ya amsa wannan karon. Kuma duk Najeriya kowa ya shaida kan yadda aka samu kwanciyar hankali a Zamfara.

Yanzu ana zuwa kasuwanni da gonaki tare da Fulani da sauran mutanen gari ba tare da tsangwama ba. ’Yan bindiga da kansu suka rika kawo makamansu, suna neman afuwa da yafiya. Sannan mutanen gari suka rika yafe musu, ana raha ana dariya.

Domin magance matsalar rashin aikin yi da jahilci, sai Gwamna Matawalle ya biya bashin da hukomomin jarrabawar sakandare ke bin jihar baki daya, aka sako wa yara sakamakon jarrabawarsu domin su ci gaba da karatu. Sannan ya farfado da Kamfanin Takin Zamani na Zamfara domin samar wa matasa aikin yi.

Haka Gwamnan ya kaddamar da aikin gina filin jirgin sama a Gusau, wanda zai samar da ayyyukan yi ga mutanen gari, sannan zai saukake zirga-zirga ga mutanen jihar. Babban abin burgewa game da Matawalle shi ne yadda ya dage wajen tabbatar da cewa lallai an samu zaman lafiya.

A bikin Sallar da ta gabata, an gabatar da bikin Sharo na Fulani a cikin Gusau, inda Fulanin suka taru, sannan Gwamna da Mataimakinsa da sauran manyan masu rike da mukaman gwamnati suka halarci taron. Kuma aka yi wasa aka tashi lafiya. Sannan daga bisani aka sanar da cewa za a fara koyar da harshen Fulatanci a makarantun jihar, domin cire wa yara masu tasowa kiyayyar Fulanin ko harshensu. Yanzu dai zaman lafiya ya samu, kuma mutane sun fara cin moriyar dimokuradiyya kamar yadda ya kamata.

A karshe ina kira ga Gwamna Matawalle ya ci gaba da ayyukan da ya fara, domin mutane suna tare da shi. Allah Ya sa zaman lafiya ya daure. Sannan jihohin Sakkwato da Katsina da Kaduna Allah Ya ba su zaman lafiya, Ya amintar mana da hanyoyinmu da garuuwanmu baki daya.

Mubarak Dangarba, 08022582833