✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwana 1 bayan gobarar kasuwa, wata ta sake tashi a Jami’ar Katsina

Gobarar ta tashi sakamakon haduwar wutar lantarki da aka samu a na'urar sanyaya wuri.

Kwana da iftila’in gobarar da ta yi sanadin salwantar dukiyoyin mutane a babbar kasuwar jihar Katsina, wata gobarar ta sake tashi a jami’ar Umaru Musa Yar’adua ita ma dake Katsinan.

Sai dai Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar,  Abdulhamid Danjuma, ya ce gobarar ba wata babba ba ce.

Danjuma ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Talata.

A cewarsa, gobabar ta tashi ne a ginin Majalisar Gudanarwar Jami’ar, amma ba ta yi wata gagaruwamar barna ba.

Ya kara da cewa gobarar ta tashi sakamakon haduwar wutar lantarki da aka samu a wata na’urar sanyaya muhalli.