Kwana da iftila’in gobarar da ta yi sanadin salwantar dukiyoyin mutane a babbar kasuwar jihar Katsina, wata gobarar ta sake tashi a jami’ar Umaru Musa Yar’adua ita ma dake Katsinan.
Sai dai Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Abdulhamid Danjuma, ya ce gobarar ba wata babba ba ce.
- COVID-19: Za a yi wa shugaban Rasha rigakafi a asirce
- Bashir Dandago ya bayyana a kotu
- Ma’aikata sun garkame majalisun dokokin Yobe da Jigawa
- Bayan kai masa hari, Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri Buhari
Danjuma ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Talata.
A cewarsa, gobabar ta tashi ne a ginin Majalisar Gudanarwar Jami’ar, amma ba ta yi wata gagaruwamar barna ba.
Ya kara da cewa gobarar ta tashi sakamakon haduwar wutar lantarki da aka samu a wata na’urar sanyaya muhalli.