✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin PCNI ya ba Adamawa tallafin kayan asibiti na Naira miliyan 400

A ranar 2 ga Fabrairun nan ne, Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI, Alhaji Tijjani Tumsah ya mika wa Jihar Adamawa tallafin kayan aikin asibiti da magunguna…

A ranar 2 ga Fabrairun nan ne, Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI, Alhaji Tijjani Tumsah ya mika wa Jihar Adamawa tallafin kayan aikin asibiti da magunguna na Naira miliyan 400 domin raba wa asibitocin da rikicin manoma da makiyaya ya shafa a jihar. Mataimakin Gwamnan Jihar Adamawa, Mista Martins Babale, wanda ya amshi tallafin, ya nuna godiyarsa ga Kwamitin PCNI saboda karimcinsa kuma ya sha alwashin cewa za a rarraba kayayyakin a wuraren da suka cancanta a fadin jihar.