✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin Limaman Abuja ya gargadi mambobinsa kan kai siyasa masallaci

Kwamitin Limaman Abuja, ya gargadi limamai su guji kai batun siyasa masallaci. Kwamitin ya bayyana haka ne taron bita na yini biyu da ya shirya…

Kwamitin Limaman Abuja, ya gargadi limamai su guji kai batun siyasa masallaci. Kwamitin ya bayyana haka ne taron bita na yini biyu da ya shirya ga limaman inda a ka gabatar da laccoci a kan al’amuran shugabanci da na al’umma.

Daga cikin kudirorin da taron ya cimma kamar yadda Sakataren Kwamitin, Malam Is’hak Zango ya gabatar wa Aminiya, sun hada da bukatar limamai su nisanci daukar kamfe na siyasa ga jam’iyya ko ’yan takara zuwa mimbarorinsu na wa’azi, maimakon haka an hore su da su fadakar da al’umma a kan zaben ’yan takara nagari, ba tare da fifita jam’iyya ba don magance rabuwar kai.

Sama da limamai 300 ne daga yankin Abuja da kewaye suka halarci bitar inda manyan malamai da suka hada da Shugaban Kwamitin, Sheikh Tajuddin Bello Limamin Masallacin Juma’a na Wuse Zone 3, Abuja da Sheikh Muhammad Kabir Adam na Masallacin Kasa na Abuja, suka gabatar da laccoci.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Masallacin Juma’a na Wuse Zone 3 Abuja, a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata ya samu halartar manyan baki ciki har da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello da Shugaban Hukumar Kwatsam Kanar Hameed Ali (mai ritaya), a ranar kaddamarwar.

Haka taron ya tattauna a kan al’amuran da suka shafi tsaro da matsalar cin hanci, inda aka shawarci limamai su yunkura wajen kafa wata sana’a ta hadin gwiwa ta fuskar halal, don mai da su masu dogaro da kai wajen magance bukatunsu. Sannan ya ja hankalinsu kan su kasance masu wadatar zuci a kan abin da Allah Ya huwace musu na abin hannu da kuma kauce wa gabatar da bukata ga wadanda suke jagoranta ta kai-tsaye ko kuma a fakaice, inji sanarwar taron.

Jagororin wasu hukumomin tsaro da suka hada da na sojan kasa da ’yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya da Shugaban Hukumar EFCC, duk sun aika da wakilansu a ranar bude taron inda suka bayyana sakonsu na fatan alheri.