✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamitin ayyuka ne kaɗai zai iya dakatar da Ganduje a APC — Kana

Kana, ya ce akwai matakai da ake bi kafin dakatar da duk wani ɗan jam'iyyar.

Mai Bai Wa Jam’iyyar APC Shawara Kan Harkokin Shari’a, Abdulkarim Kana, ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa (NWC) ne, kadai ke da alhakin dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Kana, ya bayyana haka ne yayin hira a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Ya yi wannan martani ne kan dakatarwar da wasu shugabannin jami’yyar APC a mazaɓar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, suka yi wa shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Shugabannin jam’iyyar a mazaɓar sun dakatar da Ganduje, bisa zargin cin hanci da rashawa, a lokacin da yake gwamnan Kano.

Sai dai shugabancin jam’iyyar APC na Jihar Kano, ya soke dakatarwar tare da korar waɗanda suka dakatar shi daga jam’iyyar.

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, ta jaddada hukuncin dakatarwar da aka yi wa Ganduje na wucin gadi, zuwa lokacin da za ta kammala shari’a kan zarge-zargen da ake masa.

Alkalin babbar kotun da ke Kano, wanda tun farko ya tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje, ya janye dakatarwar da kotun ta yi wa tsohon gwamnan na Kano a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

Da yake magana a ranar Litinin, Kana ya ce babu wata ƙungiya a jam’iyyar da ke da hurumin dakatar da kowane ɗan jam’iyyar face kwamitin ayyuka na jami’yyar na ƙasa.

A cewarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar, dole ne a bi wasu matakai kafin zartar da irin wancan hukunci da aka ɗauka a kan Ganduje.

“Duk waɗannan hanyoyi dole ne a kare su kafin zartar da irin wannan hukunci idan an kammala bincike, babu wata ƙungiya a APC da ke da hurumin dakatar da duk wani ɗan jam’iyya da ake bincike a kansa sai kwamitin ayyuka na ƙasa,” in ji shi.

Kana, ya ce waɗanda suka dakatar da Ganduje babu wanda ya san da zamansu a jam’iyyar.

Ya ce: “…Na san wasu ɗaiɗaikun mutane, su ba shugabannin mazaɓar Ganduje ba ne, kuma ba shugabannin unguwanni ba ne. Tun da farko, lokacin da waɗannan bayanai suka bayyana a gare mu, abu na farko da muka yi shi ne bincike kuma muna da hanyar da za mu tabbatar da ko akwai waɗancan zarge-zarge.

“Wannan babban zargi ne, cewa wata ƙungiya a jam’iyyar za ta ɗauki wannan mataki. Mun gudanar da bincikenmu, kuma ba a ɗauki lokaci mai tsawo ba muka gano waɗanda suka ce sun dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, ba ‘ya’yan jami’yyar ba ne a mazaɓar Ganduje ba.

“Ofishina bai tsaya karɓar rahotanni daga ɗaiɗaikun mutane dangane da sahihancin wannan zargi ba, mun gayyaci kwamitin ayyuka na jiha tare da na mazaɓa zuwa Abuja domin tattaunawa da su, kuma na dage sai sun zo da katin shaida da kuma katin zaɓensu.

“Lokacin da suka zo da katin shaidarsu, sai muka gano cewa waɗanda suka bayyana a talabijin kan wancan zarge-zarge ba su ne a jikin katin shaidar ba, wannan lamari yana da girman gaske.

“Hakan ne ya sanya ba mu ɓata lokaci ba wajen sanya jami’an tsaro cikin lamarin domin gudanar da bincike kan dalilin da ya sa waɗannan mutane za su yi wannan zarge-zarge, ‘yan damfara ne, abin da suke yi kenan. Kuma mun karɓi koke daga shugabannin mazaɓar na gaskiya wanda muka aike wa ‘yan sanda, yanzu maganar tana gaban ‘yan sanda domin gudanar da bincike.”